George Weah: Daga tauraron kwallon kafa Liberiya zuwa shugaban kasa
Tarihinsa za a iya yin sinima da shi wata rana, dan talaka mahaifinsa mai aikin kanikanci, ya tasa buga kwallon kafa a nahiyar Turai. Yanzu kuma a zabeshi a matsayin shugaban kasar Liberiya. .
Tauraron kwallon kafar da ya yi tashe
A wajen Liberiya George Weah an san shi a matsayin dan kwallon kafa. A lokacinsa ya kasance dan wasan gaba mafi gwanancewa a duniya. Kwallon kafa ya taimaka wa Weah kaucewa shiga cikin rayuwa mai wahala. Dan mai aikin kanikanci ya girma a cikin unguwanin marasa galihu, zuri'arsu ta samu kanta cikin kangin talauci bayan rasuwar mahaifinsa. Sai dai wata kungiyar kwallon kafa ta tantance shi.
Daga Kamaru zuwa Faransa
George Weah shi ne dan wasan da ya fi zura kwallo a raga a Liberiya a 1987 inda ya buga a cikin gaggararren klub din na Eleven, a lokacin da klub dinsa ya kara da na Tonnerre Younde, shugabannin klub din sun gano basirarsa suka kuma dauke shi. Sai dai a can rayuwa ta yi wa Weah wahala. Saboda ba ya jin harshen Faransanci da ake yin magana da shi a Kamaru don yin hulda da sauran 'yan wasan.
Ya shahara ya kuma samu daukaka a Turai
Bayan watanni shida a Kamaru, Weah ya isa klub din Faransa na AS Monaco a 1988. Wannan shi ne farkon daukakarsa cikin nasara a Turai inda ya buga kwallon kafa a klub daban-daban a Turai. An zabe shi a matsayin gwarzon dan wasa na shekara na Afirka. Mai horas da 'yan wasan Milan, Arrgo Sacchi ,ya yi bayani a kansa: ''A kowace bajinta da ya yi a lokacin wasannin za ka ga wani abu sabo.''
Rashin samun nasarar buga kwallon kafa na cin kofin duniya
Duk da shahara da kuma sunan da George Weah ya yi a Turai, Amma Burinsa na shiga gasar duniya ta kwallon kafa bai taba cika ba. A shekara ta 2002 Liberiya ta kasance daga cikin kasashen da suka halarci gasar kofin nahiyar Afirka a Mali. Weah na daya daga cikin masu horas da 'yan wasan, sai dai ya yi marabus bayan da aka fitar da Liberiya a wasannin tun zagayen farko.
Yaki da talauci da kuma take hakin bil Adama
Weah ya yi amfani da nasarorinsa domin taimaka wa marasa karfi. A 1997 Asusun yara kanana na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya nada shi wakili na musammun na wasanni. Weah ya ba da taimako ga kungiyoyin agaji, abin da ya kara janyo masa farin jini a kasarsa wacce yakin basasa ya janyowa nakasu.
Rayuwar iyali
George Weah na auren Clar, wata 'yar Amirka 'yar asilin Jamaica. Suna da ya'ya uku. Dansa na farko ya gaji ubansa yana buga kwallon kafa. Weah ya saka wa gidan talabijan mallakarsa sunan matasarsa ''Har kullum tana goyon bayana tare da bani kuzarin cewar na yi wa kasata wani abu'' kamar yadda ya bayyana a shekarar 2008 ga wata jaridar Jamus Stern.
2005: Wata bazata ta samun matsayin shugaban kasa
George Weah ya samu sauye-sauye bayan ya bar kwallon kafa. Ya koma dan siyasa, a shekara ta 2005 lokacin zaben shugaban kasa na Liberiya bayan yakin basasa.Ya zo na biyu a zagaye na biyu na zaben shugaban kasa. Wanda Ellen Johnson-Sirleaf ta samu nasara da kashi 59,4% yayin da shi kuma ya samu kashi 40,6% cikin dari.
Yayi aiki a majalisa
Bayan fafutukarsa ta zama mataimakin shugaban kasa a shekara ta 2011, Weah ya samu kujerar dan majalisa dattawa a shekara ta 2014. Weah ya doke abokin adawarsa, Robert dan shugabar kasar Johnson-Sirleaf inda ya samu kishi 78% cikin dari na kuri'un da aka kada. Sai dai kafofin yada labarai sun ce bai taba zuwa zaman majalisar ba, ko a amince da wani kudirin doka tare da shi.
2017: Yunukuri na biyu
George Weah ya kasance dan siyasa jajirtacce. a shekara ta 2017 ya sake tsayawa takara a zaben shugaban kasa. Sai dai shawararsa ta zaben Jewel Taylor a matsayin mataimakiyarsa ya ba da takaici ga jama'a a Liberiya da kuma kasashen duniya. Ita dai tsohuwar matar shugaban kasar Liberiya ne Charles Taylor, wanda ya amince da tafka laifukan yaki a shekara ta 2012.
Sabon shugaban kasar Liberiya
George Weah ya samu nasara a zagayen farko na zaben shekara ta 2017. Kafin a dage zaben bayan korafin daya daga cikin 'yan takarar na tafka magudi. Weah ya lashe zagaye na biyu na zaben a ranar 26 ga watan Disamba na shekara ta 2017 da kashi 61,5% cikin dari na kuri'un da aka kada, yayin da tsohon mataimakin shugabar kasa Joseph Bokai ya samu kashi 38,5%.