1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

George Weah na fuskantar adawa

Abdul-raheem Hassan
October 24, 2017

Jam'iyyar Liberty ta bukaci hukumar zaben kasar Laberiya da ta soke nasarar sakamakon zaben shugabanan kasa da ya ba wa tsohon dan wasan kwallon kafa George Weah damar tsallakawa zagaye na biyu.

https://p.dw.com/p/2mNq8
Fussball WM 2010  Qualifikationsgruppen - Auslosung Georg Weah
Hoto: picture-alliance/dpa/Pressefoto ULMER/M. Ulmer

Zargin magudi da aringizon kuri'u da jam'iyyar Liberty ke wa wasu jami'an hukumar zaben Laberiya, na haifar da shakku da fargaba a zukatan al'umma kan makomar sakamakon zaben baki daya, zaben da ake cike da fatan kawo sauyi mai nagarta ga turbar dimukaradiyyar kasar ta hanyar musanyar mulki tsakanin fararen hula.

Kawo yanzu dai babu martani daga bangaren hukumar zaben kasar mai zaman kanta, kan irin tuhumar ba daidai ba da ke bukatar soke sakamakon zaben. A ranar 25 ga watan Oktoba ne hukumar zaben ke shirin bayyana sakamakon zagayen farko na zaben shugaban kasar a hukumance.

A ranar bakwai ga watan Nuwamba ne George Weah tsohon dan kwallon kafa, zai fafata a zagaye na biyu tare da abokin karawarsa mataimakin shugaban kasa mai ci a yanzu Josep Bokai. Kungiyoyin sa ido na kasa da kasa da suka sheda yadda zaben na Laberiya ya gudana, ba su bayyana rashin tsari a zagayen farko na zaben.