1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cutar sukari na mata masu juna biyu

Rahmatu Abubakar Mahmud
March 12, 2019

Rukunin kwararru a fannin kula da lafiyar mata sun nuna fargaba dangane da yiowuwar mata masu juna biyu su kamu da cutar sukari lokacin da suke dauke da juna biyu, wanda kan jefa uwa da ma jinjirin cikin hatsari

https://p.dw.com/p/3Eqj0
Symbolbild Afrika Schwanger
Hoto: imago stock/Gallo Images

A dai duk lokacin da mace ke dauke da juna biyu dai tana cikin hatsarin hawan sukari domin kuwa yawan cin abincinta na karuwa ne kuma motsa jiki sai dada raguwa yake.

Kenan akwai yiwuwar kamuwa  da cutar sukari a wannan lokacin. A cewar wani likitan kula da mata cutar sukari na masu juna biyu dai kan haifar da damuwa da dama.

Tun farko farkon daukar ciki za'a iya rasashi sabili da cutar sukari na masu juna biyu, kuma yana sa haifar jinjiri mai girma fiye da yadda ya dace. Don haka sukan fuskanci matsaloli gurin haihuwa, a dayan hannu ma jinjirin kan fuskanci matsalololi na kashi da zuciya ko na hankali.

Kiyasi na nuna cewar kashi 10 daga cikin dari na mata masu juna biyu da ke zuwa babban asibitin Korle-bu domin kula da lafiyarsu, na dauke da cutar sukari ta masu juna biyu kuma akwai yiwuwar kamuwa da cutar ta type 2 nan gaba cikin rayuwarsu.

A cewar daya daga cikin rukunin binciken dai cutar suga ta masu juna biyu za a iya magance shi ko kuma kwantar da shi idan har su masu juna biyun zasu kula da cin abincinsu tare kuma da aiwatar da wasannin motsa jiki da suka dace da su.