1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mahawara kan kasafin kudin 2019

November 22, 2018

Bangaren gwamnatin Ghana ya kwatanta kasafin kudin badi a matsayin mafi inganci a kan al’amuran kasar, bangaren marasa rinjaye kuwa kwatanta shi suka yi a matsayin wanda zai kara jefa rayuwar jama’a cikin matsi.

https://p.dw.com/p/38iSC
Ghana oppositioneller Kandidat Nana Akufo-Addo
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Muhawarrar ta fara ne a lokacin da wani dan majalisar da ke wakiltar mazabar New Juabeng South kuma mai jagorantar kwamitin da ke kula da harkokin kudi na majalisar Mark Asibey Yeboah, ya zargi NDC da lalata lamuran tattalin arzikin kasar a lokacin da NPP ke mulki, ko da yake gwamnatin NPP ta cimma nasarar cika alkawarinta na karfafa tattalin arzikin kasa a tsawon watanni 22. Yana mai cewa: ko kadan babu wani kudirin bunkasa rayuwar jama'a da gwamnatin baya za ta iya yin alfahari da shi, idan aka dubi adadin yawan jama'a, in kuma suna gardama su nuna mana. Amma a halin yanzu kwararrun ne ke jan akalar wannan gwamnati, domin tun bayan dawowarmu mun nuna kwazonmu ta hanyar maido da komadar tattalin arzikinmu a kan hanyar da ta dace, haka kuma muka bunkasa ababan more rayuwa, yanzu abinda ya rage shi ne, nasarorin da muke hankoron cimma wa a gaba.

Bangaren marasa rinjaye na adawa da wannan ikirarin, lamarin da ya janyo kace-nace a majalisar, a kan abinda marasa rinjayen ke kwatantawa da yaudara, da kuma sabawa wasu dokokin da ke tabbatar da yin tattalin kudaden gwamnati da na arzikin albarkatun man fetur, kamar su haramta kashe sama da kaso 70% daga wadannan kudade, wajen aiwatar da harkokin kudi.Kakakin marasa rinjaye a kan harkokin kudi Cassiel Ato Forson, wanda ke cewa: duk da cewa babu wani kwakkwaran mataki da aka bijiro da shi, kuma gashi yanzu gwamnati na cewa kudaden shiga ta fuskar haraji zai tsaya kan kaso 13%, wannan ba komai bane face tafiyayyen bashi, domin idan shekarar bara ba ta tabuka komai ba kuma a cikin kasafin naku na badi kun shaida cewa kun gaza, tun kafin akai ga shiga.

Ghana Wahlkampf Nana Akufo-Addo
Hoto: dapd

Biyo bayan wannan dai ministan yada labarai Kojo Oppong Nkrumah, ya zargi bangaren marasa rinjayen da munafurci tare da gaddamar cewa gwamnatin NDC da ta shude ta tafka mummunar barna, wacce gwamnatin mai ci ke kokarin magancewa, dan samarwa jama'ar kasa ayyuka. Shi dai a nasa bangare tsohon mataimakin ministan kudi Fiifi Kwetey, shugabancin Akufo Addo, na kwatanta tsantsar rashin kwarewa wajen gudanar da sha'anin tattalin arzikin kasar nan.

Fiifi Kwetey, ya kara da cewa: a cikin gabatar da wannan kasafi ministan kudi ya sha maimaita iyakar kwarewar wannan gwamnati, inda yin hakan alama ce da ke nuna cewa duk ikirarin sa labari ne, irin na kanzon kurege.

Har ila yau dai, marasa rinjaye sun kara da barazanar kauracewa majalisar kan rattaba hannu kan kudirin wannan kasafi, tare da daukar matsayin cewa, yin la'akari da alkalluma na bayanan bashin kasar, wanda ke tsaye a kan sidi biliyan 170.8 a yanzu, wanda ke nufin cewa kowane dan kasar na dauke da bashi akalla sama da sidi 5,000 har ma da jarirai.