1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Girgizar kasa ta afku a Afirka ta Kudu

August 5, 2014

Mace daya ce aka tabbatar da mutu yayin da mahakan ma'adinai suka makale a karkashin kasa sakamakon girgizar kasa da ta afku a garin Orkney na Afirka ta Kudu.

https://p.dw.com/p/1Cp67
Hoto: Gilberto Fontes

Wata girgizar kasa da karfinta ta kai maki biyar da digo 3 a ma'aunin Richter ta afku a birnin Orkney na kasar Afirka ta Kudu inda ta kashe mutun guda. Jami'an agaji sun bayyana cewar wani gini da ya rifta ne ummal aba'isan mutuwar ita matar a wannan bala'i daga indallahi a yankin Arewa maso yammacin wannan kasa.

Sannan kuma kakakin Kungiyar agaji ta ER24 Luyanda Majija ta bayyana wa manaima labarai cewar dimbin masu hako ma'aidinai sun makale a ramukan hako arzikin na karkashin kasa, ba tare da yin wani karin haske ba.

Wannan girgizar kasar da ta afku a daidai karfe 11 da rabi agogon Najeriya da Nijar ta girgiza manyan gine-gine da dama a Johannesburg cibiyar cinikayyar Afirka ta Kudu. Sannan kuma a ji ruguginta a kasashen Mozambik da kuma Botswana.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Usman Shehu Usman