1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Gobara ta halaka fursunoni 38 a Burundi

December 7, 2021

Gobara ta yi ajalin fursunoni 38 a gidan kaso da ke birnin Gitega da ke zama cibiyar siyasar kasar Burundi. Mataimakin shugaban kasar ta Burundu Prosper Bazombanza ya ce akwai karin fursunoni 69 da gobarar ta raunata.

https://p.dw.com/p/43wtS
Burundi Gitega Angeklagte in grüner Kleidung
Hoto: Getty Images/AFP/Stringer

Ma'aikatar kula da harkokin cikin gida ta kasar Burundi ta ce matsalar lantarki ce ta haifar da gobarar a wannan Talata, lamarin da ya tayar da hankulan mutanen wannan karamar kasa da ke gabashin Afirka. Rahotanni sun ce sai da fursunonin suka yi sa'o'i biyu suna ci da wuta kafin ma'aikatan agaji su halarci wurin.

A watan Agustan da ya gabata ma dai an samu gobara a gidan yarin da lokacin ma hukumomi suka ce fashewar abubuwan lantarki ce ta haifar da ita. Gidan kason na Gitega shi ne na uku mafi girma a Burundu kuma ya zama fitaccen wuri da ake zaunar da fursunonin siyasa. Sai dai ya jima a cunkushe, inda kawo karshen watan da ya gabata fursunoni 1500 ke a cikinsa maimakon mutane 400 da aka tsara ajiyewa a gidan mazan.