1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Guguwar siyasa ta kaɗa a Johannesburg

January 29, 2014

A ƙasar Afirka ta Kudu, jam'iyyar ANC mai mulki za ta fiskanci babban ƙalubale a zaɓen bana, inda Mamphela Ramphele za ta ƙalubalanci Jacob Zuma.

https://p.dw.com/p/1A2F3
Mamphela Ramphele, afrikanische Aktivistin
Mamphela RampheleHoto: picture-alliance/dpa

Yayin da jam'iyyun siyasa a ƙasar ta Afirka ta kudu, ke shirin tinkaran zaɓen da ke tafe. Ba zato ba tsammani dai sai fitacciyar jam'iyar adawa Demokratik Allianz wanda aksarin magoya bayanta fararen fata ne, ta haɗe da jam'iyyar adawa ta baƙaƙen fata, inda kuma ta amince baƙin fata Mamphela Ramaphele ta kasance yar takaranta na shugaban ƙasa a zaɓen bana.
Jam'iyyar ta ANC dai ita ce ke mulkin ƙasar tun kawo ƙarshen mulkin wariyar jinsi, wanda marigaye Mandela ya jagoranta. To amma tabbas wannan shi ne karo na farko da za ta fiskanci babban ƙalubale. Mamphela Ramphele yar shekaru 67 da haifuwa, wanda likitace, kana tsowar manaja a Bankin Duniya, fitacciya ce a siyasar Afirka ta Kudu. Inda kuma tuni ta nuna cewa za ta iya ƙwace mulki a hannun shugaba Jacob Zuma, tana mai cewa.
"Mu gwamnati ce mai jiran gado, mu wakilai ne na miliyoyin 'yan ƙasar Afirka ta kudu, waɗanda suka yi imani da alƙawarin cewa, mune ke da damar mulki na jam'iyyun daba-daban a demokraɗiyyance"
Wannan sanarwar haɗewar babbar jam'iyyar adawa da fararen fata suka yi mata katutu da kuma ta baƙaƙen fata, a yanzu ya sa 'yan ƙasar Afirka ta Kudu na ta maida martani mabambanta. Kamar yadda wannan martar ta yi tsokaci.
"Zan kaɗa kunne, na saurari abinda suke faɗa, domin fahimtar ainihin tsarinsu. Minene manufarsu da haɗewar, ina mamaki idan ba wai kawai sabuwar fiskace aka kawo, wannan lamarin ba saban ba ne"
Suma dai masu sharhi na cewa , wannan ba komai bane illah kawai jam'iyyar da fararen fata suka yi wa katutu, so ta ke ta samu amincewa daga baƙaƙen fata. Abinda da ta rasa duk da girman da ta ke da shi.
"Demokratik Allianz ta kai ƙololuwa idan dai girma ta kesu, ta na neman kawo wa kanta halarci ne, wanda ta rasa sakamakon kallon da ake yi mata, a matsayin jam'iyyar fararen fata, iya batun kenan"
Tun bayan kawo ƙarshen mulkin wariyar jinsi shekaru 20 da suka gabata, kawo yanzu sai dai 'yan ƙasar Afirka ta Kudu sauyin da suke gani bashi da yawa, rashin aikin yi da talauci yana ƙaruwa, inda masu arziki ke ƙara arzurta, yayinda talakawa ke ƙara durƙushewa. Masu zaɓen jam'iyyar ANC ba su ga wani zaburar tattalin arziki ba, shi ma kansa shugaba Jacob Zuma ya samu kansa cikin rigingimun cin hanc, da taɓargaza ta lalata da mata.
Ramphele ta na kallon kanta a matsayin yar siyasar Afirka ta Kudu baƙar fata, wanda ita ce kaɗai cikin fitattatun da suka yi yaƙi da mulkin wariyar jinci, kuma basa cikin jam'iyyar ANC.

Nelson Mandela Beerdigung Beisetzung Demonstranten Demonstration
Matasan Afirka ta KuduHoto: Reuters
Jacob Zuma Präsident Süfafrika November 2012
Jacob ZumaHoto: Stringer/AFP/Getty Images

Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Mohammad Nasiru Awal