1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Guterres: Barazanar tsaro na karuwa a Mali

March 6, 2019

Majalisar Dinkin Duniya ta ce lamuran tsaro na ci gaba da ta'azzara a kasar Mali, sakamakon karuwar hare-haren ta'addanci a kan sansanonin soji da kuma na jami'an kiyaye zaman lafiya na gida da waje.

https://p.dw.com/p/3EY3D
Schweiz Genf UN Menschenrechtsrat Antonio Guterres
Hoto: picture-alliance/KEYSTONE/S. Di Nolfi

Sakatare Janar na Majalisar ta Dinkin Duniya Antonio Guterres, na cewa barazanar 'yan bindigar da ke sheke aya a Mali na ci gaba da yaduwa ne musamman daga yankin tsakiya zuwa arewacinta.

Hakan kuwa a cewarsa na matukar durkusar da kokarin da ake yi na ganin an cimma yarjejeniya ta zaman lafiya da su masu tayar da kayar bayan.

Cikin wannan watan ne dai kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniyar ke shirye-shiryen kai ziyara kasar ta Mali, dangane da yiwuwar tsawaita wa'adin zaman dakarun kiyaye zaman lafiya na MINUSMA da ke can.