1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Girka ta gabatar da wata doka ga Majalisa

Salissou BoukariJuly 14, 2015

Hukumomin kasar Girka sun shigar da wata ayar doka kan batun sabin canje-canjen da kasar zata aiwatar wanda abokan huldarta na Turai suka bukata.

https://p.dw.com/p/1FyZg
Hoto: Reuters/E. Vidal

Gwamnatin kasar Girka ta gabatar da wata ayar doka a gaban majalisar dokokin kasar kan batun sabin canje-canjen da abokan hultarta na Turai suka bukata a cewar wata majiya ta majalisar dokokin ta Girga. Wannan ayar dokar ta zo ne kwanaki biyu kacal bayan cimma yarjejeniyar da aka yi a birnin Brussels tsakanin kasar ta Girka da sauran kasashe masu amfani da kudin Euro, kan batun wani sabon tallafin kudade ga kasar ta Girka. Wani kwamitin 'yan majalisun ne dai zai yi nazarin ayar dokar kafin a yi mahawara a kanta a zauran majalisar domin samun amincewar 'yan majalisun cikin gaggawa.