1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Gwamnatin Kwango ta yi watsi da kiran sake zaben kasar

Zainab Mohammed Abubakar
December 28, 2023

Jamhuriyar Demokuradiyyar Kwango ba za ta sake gudanar da zaben kasa baki daya da aka gudanar a makon da ya gabata ba, kamar yadda 'yan adawa suka nema.

https://p.dw.com/p/4afuh
Hoto: John Wessels/AFP

Kakakin gwamnatinkasar Kwango Patrick Muyaya ya sanar da hakan duk da kiran da 'yan adawa suka yi na a sake gudanar da zaben mai cike da takaddama.

Kwarya-kwaryar sakamakon zaben na ranar 20 ga watan Disamba a Jamhuriyar Demokuradiyyar Kwango, ya nuna shugaba Felix Tshisekedi yana kan gaba da yawan kuri'u a kan 'yan adawa.

Tashe-tashen hankulan da ake fama da su a kan zaben na barazanar kara dagula lamura a Kwangon, wadda tuni ke fama da matsalar tsaro a yankunan gabashin kasar, da ke da dumbin arzikin ma'adanai da karafa na masana'antu a duniya.

'Yan sanda sun yin amfani da karfi wajen tarwatsa wata zanga-zangar adawa da aka haramta gudanarwa a Kinshasa babban birnin kasar, in da jama'a suka yi dafifi don nuna rashin gamsuwa da yadda aka gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki, da a cewarsu ke cike da kura-kurai.