1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Masar na fuskantar ƙalubale

November 19, 2013

Jami'an tsaron ƙasar Masar sun yi amfani da ƙarfi wajen wargaza masu nuna adawa da gwamnatin ƙasar.

https://p.dw.com/p/1AL0z
Hoto: picture-alliance/dpa

Jami'an tsaron Masar sun fasa dandazon da matasan juyin-juya hali suka shirya a dandalin Tahreer wanda sojoji suke wa ƙawanya tun bayan tunɓuke Mohamed Mursi daga madafun kin ƙasar ta Masar.Jami'an tsaron sun harba hayaƙi mai saka hawaye kan matasan da ke rera taken nuna ƙyama ga babban hafsan sojin ƙasar Janar Abdulfatah Al-Sisi.

Wannan ya auku ne a yayin da suke juyayin tunawa da cika shekaru biyu da artabun da aka yi kan titin Muhammad Mahmud da ke ɗaura da dandalin Tahreer, tsakanin sojojin ƙasar gami da jami'an tsaro a gefe ɗaya, da matasan juyin-juya hali a ɗaya gefen, lamarin da ya kai ga hallaka matasa 48 a wanccan lokacin, bayan da ƙungiyoyi masu ra'ayin Islama a wanccan lokacin suka siffanta matasan da 'yan banga masu tayar da tarzoma, lamarin da ya sanya matasan a wannan karon yin hannun riga da 'yan uwa Musulmi da sojojin ƙasar da kuma waɗanda suka kira birbishin muƙarraban tsohon Shugaba Hosni Mubarak. Kuma ga abin da suke cewa:

Ägypten Jahrestag der tödlichen Zusammemstösse in Kairo
Hoto: picture-alliance/dpa

"Taken da muke ɗagawa a yau shi ne, sai mun ga bayan duk wanda ke da hannun wajen kashe matasan juyin-juya hali, sawa'un membobin majalisar wucin gadin soji ne, ko kuma yaran Mubarak ne, ko 'yan uwa Musulmi waɗanda suka yaye mana baya a yayin gwagwarmaya har aka kakkakashe mu."

Bugu da ƙari, matasan sun tunɓuke dogon yaron da firaministan ƙasar Hazim Biblawi ya gina don abin da ya kira, tunawa da mazan jiyan da suka kwanta dama a yayin juyin-juya hali na ɗaya da na biyu da akai a kasar ta Masar. Matasan sun jajirce kan cewa, juyin-juya hali daya tilo a kai a ƙasar, wanda ya kai ga kifar da Mubarak, amma kifar da Shugaba Mursi duk da saɓanin da suke da shi, juyin mulki ne ƙarara da ya mayar da hannun agogo baya, a hankoran da 'yan ƙasar ke yi na samun 'yanci da walwala gami da girka tafarkin demokraɗiyya.

A gefe ɗaya cikin dandalin, ɗarurruwan magoya bayan shugaban sojojin ƙasar Abdul-fatah Al-Sisi da ke samun kariyar jami'an tsaro sun yi ta rera take nuna goyon bayansa, a ranar da suka ce, ta yi dai dai da ranar haihuwarsa.Tun bayan kifar da Mursi magoya bayan shugaban sojojin suke ya yi tazarce.

Egypt's Army Chief General Abdel Fattah al-Sisi attends a meeting with Egypt's interim President Adly Mansour, Russia's Defence Minister Sergei Shoigu and Foreign Minister Sergei Lavrov (not pictured) at El-Thadiya presidential palace in Cairo, November 14, 2013. Sisi hailed a new era of defense cooperation with Russia on Thursday during a visit by Russian officials, signaling Egyptian efforts to revive ties with an old ally and send a message to Washington after it suspended military aid. REUTERS/Amr Abdallah Dalsh (EGYPT - Tags: POLITICS MILITARY)
General Al SisiHoto: Reuters

A ɗaura da haka, magoya bayan hamɓararren Shugaba Mursi da suka gudanar da nasu gangamin a dandalin Abbasiyya, kusa da ma'aikatar tsaron ƙasar, sun yi kira ga 'yan ƙasar da su ci gaba fafatawa cikin lumana domin bin kadin jinin waɗanda aka kashe a gwagwarmayar tabbatar da sauyi a kasar, ba tare da nuna wariya ga waɗanda suka kwanta dama ba. Kimanin mutane 900 ne dai suka hallaka a yayin fafatukar kawar da Mubarak daga kan mulki, kuma aka gurfanar da shi da mukarrabansa da wasu jami'an tsaro gaban kuliya kan alhakin kisan, sai dai har ya zuwa yanzu, ba wanda aka hukunta daga cikinsu, maimakon haka, sai aka sakosu, kana aka ci gaba da kakkame masu bin kadin wadanda aka kashen. Lamarin da ke ƙara sarkakiya a tsarin shari'a da siyasar ƙasar, musammama bayan da sabin mahukuntan ƙasar suka kashe ninkin ba ninkin waɗanda Mubarak din ya kashe.

Mawallafi: Mahmud Yahya Azare
Edita: Suleiman Babayo