1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Najeriya ta dakatar da Sanusi Lamido Sanusi

February 20, 2014

Shugaban babban bankin Najeriya ya sami labarin cewa gwamnatin ƙasarsa ta dakatar da shi a mukaminsa bisa zargin shi da wadaƙa da kuɗinsa a lokacin da yake ziyara a Nijar

https://p.dw.com/p/1BCFF
Nigeria Gouverneuer der Zentralbank Sanusi Lamido Sanusi mit Christine Lagarde
Hoto: Getty Images

Gwamnatin Najeriya ta dakatar da gwamnan babban bankin ƙasar Sanusi Lamiɗo Sanusi, kuma kafofin yaɗa labaran cikin gida sun rawaito cewa gwamnatin ta yi hakan ne bisa zarginsa da wadaƙa da kuɗin ƙasa da rashin bin ƙa'idoji

Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da gwamnnan ya zargi kamfanin man fetur ɗin ƙasar NNPC da amfani da kuɗaɗen shigan da ake samu daga man a hanyoyin da ba su dace ba.

A cewar wata sanarwar da kakakin gwamnati Reuben Abati ya fitar, ya ce Shugaba Goodluck Jonathan ya umurci Sanusi Lamiɗo Sanusi da ya miƙa ayyukansa ga mataimakiyar sa Dr Sarah Alade domin a gudanar masa da bincike.

A makon da ya gabata ne wani kwamitin majalisar dattijai ya ba da umurnin yin binciken kamfanin man fetur na ƙasar ta NNPC, bayan da Sanusi ya zarge shi da yin sama da faɗi da dala milliyan dubu 20 na kuɗaɗen shigan da ƙasa ke samu daga man fetir.

Shugaba Goodluck ya ce Dr Sarah Alade za ta cigaba da riƙe wannan muƙamin har sai an kammala gudanar da binciken.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Muhammad Awal Balarabe