1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mayakan Boko Haram na ci gaba da kaddamar da hari a Tchad

Zulaiha Abubakar
April 15, 2019

Kakakin rundunar sojojin kasar Tchad ya bayyana mutuwar 'yan ta'addan da yawansu ya kai 63 sakamakon musayar wuta tsakanin sojoji da mayakan boko haram a sansanin sojin dake Bouhama a yankin tafkin Tchadi.

https://p.dw.com/p/3GpI6
Nigeria - Boko Haram Konflikt
Hoto: picture alliance/dpa

Yayin arangamar tsakanin bangarorin biyu gomman fararen hula sun rasa ransu, da yake karin haske game da wannan al'amari ministan tsaron kasar Daoud Yaya Brahim ya bayyana cewar gwamnati ta umarci fadada bincike a yankin da abin ya faru. Yanzu haka dai mayakan Boko haram sun kara kaimin hare-haren da suke kaiwa sojojin kasar ta Tchad tun bayan sanarwar yin nasara a kan Kungiyar da mahukuntan Tarayyar Najeriya suka yi, a baya dai gamayyar rundunar sojoji daga Jamhuriyar Nijar da Najeriya da Kamaru da kuma Tchad ne suka hada karfi don yakar ayyukan kungiyar ta Boko Haram wacce ta addabi kasashen.

Wannan shine karo na bakwai da 'yan Boko Haram suka kai hari a kasar ta Tchad tun daga watan Yulin bara.