1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Haɓaka noma shi ne gaban ƙasashen Afirka

January 30, 2014

Shugabannin Ƙungiyar Tarayyar Afirka, sun jaddada shirin samar da wadataccen abinci a nahiyar, amatsayin hanya guda da ta samarda zaman lafiya.

https://p.dw.com/p/1Azn1
Afrika - Beginn des Gipfels der Afrikanische Union
Hoto: Getty Images

A yayin da shugabannin ƙasashen ƙungiyar Tarayyar Afirka suka hallara a birnin Addis Ababa, ƙungiyar ta AU da Majalisar Dinkin Duniya, duk sun fidda sanarwa neman a kawo ƙarshen tashin hankali a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Wannan shi ne jawabin buɗe taro wanda mataimakin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Jan Eliasson da kuma shugabar Hukumar Tarayyar Afirka Nkosazana Dlamini-Zuma suka faɗa. Dama dai tuni aka zaci tashin hankalin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da na Sudan ta Kudu, za su mamaye taron ƙungiyar AU na bana.

Tun daga farko dai shugaban kwamitin tsaro na ƙungiyar Tarayyar Afirka, kana shugaban ƙasar Gini Alpha konde, ya faɗawa zauren taron cewa, ƙungiyar za ta nemi taimakon kudi daga Tarayyar Turai, domin a gaggauta tura ƙarin sojojin ƙasashen Afirka 3500 izuwa ƙasar ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Konde ya kuma bayyana fatan samun agaji, a taron neman gudumawa na musamman da za'a yi ranar Asabar, bayan kammala taron shugabannin AU. Ya kuma bayyana cewa ƙasashen Aljeriya da Afirka ta Kudu da Angola, suna daga cikin ƙasashen da ake saran za su tura dakarunsu izuwa Bangui.

Nkosazana Dlamini-Zuma
Nkosazana Dlamini-ZumaHoto: picture-alliance/dpa

Shugabannin sun kuma nuna takaicinsu, bisa tashin hankali da ke ci gaba da wakkana a Sudan ta Kudu, duk kuwa da yarjejeniyar tsagaita wuta. Don haka suka buƙaci ɓangarorin biyu na shugaba Salva Kiir da na tsohon mataimakinsa Riek Machar da su tabbatar da amfani da yarjejeniyar da aka cimma.

To amma wannan fa bai hana shugabannin na Tarayyar Afirka ci gaba da tattauna batun bunƙasa noma a nahiyar. Wanda dama can shine babban jadawalin taronsu na bana. Inda shugabar Hukumar Tarayyar Afirka Nkosazana Dlamini-Zuma, ta ce.

"Dole mutabbatar cewa su ma matasa sun nuna sha'awa bisa harkar noma. Noma kan iya kasancewa hanyar zaburar da tattalin arzikinmu, kuma zai iya kasancewa hanyar haɓakar masana'antunmu. Tomma akwai hanyoyi da yawa da yakamata mu duba. Dole mutabbatar noman da muke yi, ta na samar amfani mai yawa. kana akwai buƙatar yin amfani da dabarun noma na gargajiya da mutanemu ke da fasahar amfani da su tun ɗaruruwan shekaru"

Gipfel Afrikanische Union Addis Abeba
Hoto: Reuters

Bisa ga dukkan alamau taron zai yi nasarar tattauna jadawalin nasa, domin kuwa shi ma kansa mataimakin sakatare janar na MDD Jon Eliasson, cewa ya yi, buƙatar majalisar ita ce ƙara ƙulla huldar tattalin arziki da ƙasashen Afirka.

Yace "A dai-dai lokacin da duniya ke farfaɗowa gada rikicin tattalin arziki, mun haɗu anan lokacin da ƙasashen Afirka ke haɓaka. Wannan haɓakar da ake samu, ya kamata a yi amfani da ita don bunƙasa tattalin arziki. Samar da aikin yi. A rage geɓin da ke tsakanin jama'a, domin samarwa mutane rayuwa mai inganci. MDD babbar ƙawace a wannan manufa, kuma kamar yadda ku ka sani, ƙudurorin majlisar uku na farko shi ne, "Mu Jama'a"

Wata babbar matsala da ke kawo cikas wajen ci gaban nahiyar ta Afirka dai, shi ne rashin hadin kan shugabanninta. Abin da kuma shi ma kansa Firayim ministan ƙasar Habasaha Haillemariam Desalegn, wanda a yanzu ƙasarsa ce ke shugabantar ƙungiyar AU na karɓa-karɓa, ƙiran da ya yi wa shugabbani da su haɗa kai.

"Wannan dukka ya rataya ne kan yin magana da murya guda bisa matsayin Afirka. A batutuwan da suka fi mahimmanci a yanzu. Wanda suka shafi huldar ƙasa da ƙasa, wajen bunƙasa tattalin arziki. Kawo ƙarshen talauci shine a gabanmu, shi ne kuma zai kasance babban abinda za mu sa a gaba"

A yanzu haka dai ko ba komai shugabannin ƙunguiyar Tarayyar Afirka, sun fara nuna alamun sauya yadda tarukan nasu ke gudana. Misali a baya kusan yaƙe-yaƙe ne kawai ke zama jadawali, amma a wannan karon, duk da rikicin n wasu ƙasashe na ƙungiyar ke fiskanta, amma shugabannin sun nuna alamun cewa dole sai da wadataccen abinci, kafin a hanawa mutane shiga tashin hankali. Abinda ake jira shi ne, aiwatar da abinda suka faɗa.

Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Mohammad Nasiru Awal