1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hada karfi domin tunkarar Boko Haram

June 5, 2014

Najeriya ta taimaka wa Jamhuriyar Nijar domin shawo kan matsalar tsaro a kan iyakar kasashen.

https://p.dw.com/p/1CDQo
Hoto: picture-alliance/dpa

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ba da gudumawar motocin sintiri ga jami'an tsaron kasar Jamhuriyar Nijar da zumman yaki da tabarbarewar tsaro da ake dangantawa da tsagerun kungiyar Boko Haram masu dauke da makamai.

Ana zargin 'yan kungiyar ta Boko Haram da zafafa hare-hare cikin Najeriya inda wani lokaci suke tsallaka kan iyaka domin samun mafaka. Najeriya tana kara neman hadin kai da makwabta kamar Jamhuriyar Nijar da Kamaru da kuma Jamhuriyar Cadi, domin kawar da matsalar ta Boko Haram.

Nigeria Soldaten
Hoto: picture-alliance/dpa

Ana zargin 'yan Boko Haram da hallaka mutane masu yawa cikin Tarayyar Najeriya kuma yanzu lamarin ya tabarbara lamura kan iyakar kasar da sauran kasashe makwabta kamar na Kamaru da Cadi gami da Jamhuriyar Nijar, abin da ya yi matukar tasiri wajen zagon kasa ga harkokin kasuwanci da zamantakewa. Tuni duk kasashen suka bayyana daukan matakai daban-daban domin shawo kan matsalar.

Mawallafi: Gazali Abdou Tasawa / Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal