1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hafsan sojin Aljeriya Gaid Salah ya rasu

Gazali Abdou Tasawa
December 23, 2019

Rahotanni daga Aljeriya na cewa Allah ya yi wa babban hafsan sojan kasar Janar Ahmed Gaid Salah rasuwa a wannan Litinin a sakamakon bugon zuciya. Shi ne ke ruwa da tsaki a harkokin tafiyar da kasar Aljeriya .

https://p.dw.com/p/3VGpu
Algerien | Militärchef Ahmed Gaid Salah
Hoto: Getty Images/AFP/R. Kramdi

Janar Gaid Salah wanda ya rasu yana da shekaru 79, ya kasance jigo a harkokin mulkin kasar ta Aljeriya tun daga shekara ta 1962, sannan ya taka muhimmiyar rawa wajen tilasta wa Shugaba Abdelaziz Bouteflika yin murabus a watan Aprilun da ya gabata a bisa matsin lambar masu zanga-zangar neman sauyi.

 Marigayi Janar Gaid Salah ya kuma kasance a sahun gaba na hukumar mulkin sojan da ta jagorancin kasar har ya zuwa zaben sabon shugaban kasa na ranar 12 ga wannan wata na Disemba wanda Abdelmajid Tebboune ya lashe.

 Tuni dai sabon shugaban kasar ta Aljeriya ya kaddamar da zaman makoki na kwanaki uku a fadin kasar tare da nada Janar Said Chengriha mataimakin shugaban hafsan sojan kasar a matsayin sabon shugaban hafsan soja na wucin gadi na kasar.