1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin matsin tattalin arziki a Zimbabwe

July 31, 2014

Shekara guda da sake zabar Robert Mugabe a karo na bakwai a matsayin shugaban kasa, wannan kasar ta kudancin Afirka na fuskantar matsaloli na tattali.

https://p.dw.com/p/1Cn2I
Zimbabwe Robert Mugabe
Hoto: Reuters

Kasar Zimbabwe na ci gaba da kasancewa cikin halin kaka-ni-ka-yi na matsin tattalin arziki, baya ga take hakin bil'adama da rigingimu na siyasa. A ranar 31 ga watan Julin shekarar da ta gabata ne dai aka sake rantsar da Robert Mugabe a karo na bakwai a matsayin shugaban wannan kasa da ke fama da talauci a yankin kudancin Afirka.

Har yanzu dai bata sake zani ba ga shugaban kasar ta Zimbabwe mai shekaru 90 da haihuwa. A wani jawabin da ya yi a farkon wannan wata na Yuli sai da ya jaddada cewar, ko kadan kada a yi rangwame wa fararen fatu na kasar, domin filayen kasar mallakin bakaken fatu ne. A cewar kungiyar manoman kasar dai, a yanzu haka manoma farare 150 ne kadai ke da filayen noma, bayan kwace wajen dubu hudu daga wajensu domin rabna bakaken Zimbabwe a farkon shekarun alif 2000. Kuma idan Mugabe zai aiwatar da abubuwan da ya fada, ko shakka babu suma fararen fata manoma150 din sun kusan rabuwa da filayen noma nasu.

Morgan Tsvangirai
Morgan TsvangiraiHoto: Alexander Joe/AFP/Getty Images

Robert Mugabe da jam'iyyarsa ta ZANU-PF dai sun dauki alkawura masu yawa, tun bayan da aka sake zabarsa a karo na bakwai a ranar 31 ga watan Yulin shekarata 2013, wanda ya lashe zaben da mafi rinjayen kuri'u. Duk da cewar da wannan rinjayen zai iya kawo sauyi ba tare da tsoma bakin abokin takwararsa na mulkin hadar Morgan Tsvangirai ba, babu abun da ya sauya zani a wannan kasa. Kama daga matsaloli na basussuka da durkushewar tattalin arziki da makamantansu. Jürgen Langen shi ne shugaban gidauniyar Konrad-Adenauer na nan Jamus reshen Zimbabwe...

Ya ce" cikin watanni 12 da da suka gabata, mutum zai iya bayyana halin da kasar ta ke ciki a siyasance, da cewar babu wani abun da ya sauya. Tana kara durkushewa ne a ko wace rana. A bayyane take cewar, yanzu haka tauraruwar gwamnatin ZANU-PF ta dusashe a tsakanin membominta".

Kasar ta Zimbabwe tana da tarin matsaloli. har yanzu tana kokarin farfadowa daga cikin matsalolin da ta fada a farkon shekarun 2000. A wancan lokacin dai kasar ta yi kaurin suna wajen faduwar darajar kudi, da mutuwar mutane wajen dubu hudu daga cutar kwalera, batutuwa da suka durkusar da tattalin arzikin kasar. A yanzu haka dai an shawo kan matsaloli na faduwar darajar kusi, sai har yanzu babu bunkasar tattali. Tony Hawkins, farfesan harkokin kasuwanci ne a jami'ar Harare;

" Akwai fadan cikin gida dangane da wanda zai gaji mulki. Yanzu haka shekarun Mugabe 90 da haihuwa, ba zai sake dadewa akan mulki ba, dangane da haka ne akwai fafutuka dangane da neman mukaminsa. Kuma abunda jam'iyyar Mugabe ta fi mayar da hankali akai kenan yanzu, a maimakon mayar da hanakali kan sake farfado da tattalin arzikin kasa".

Wirtschaft in Simbabwe
Harkokin tattaliHoto: JEKESAI NJIKIZANA/AFP/Getty Images

Halin da kasar ke ciki bai isa cire ta daga matsin tattali da take fuskanta ba. Amma wannan ba shi ne a gaban Mugabe ba. Yana ci gaba da rungumar tsarinsa na nuna kauna ga bakaken fatar kasar. Duk wani kamfanin ketare da ke kasar, ya zamanto wajibi ya sayerwa bakake kashi 51 daga cikin 100 na hannun jarinsa. Manyan kamafanonin hakar ma'adinai na fuskantar kalubalen da ke tattare da wannan tsari. Kamfanoni masu yawa basa muradin mika irin wannan madafan iko na hannayen jarinsu wa 'yan kasar. Daura da haka wannan tsari na kashe kwarin gwiwar masu niyyar zuba jari a cikin kasar, wadanda Zimbabwen ke nema ido a rufe domin tallafa wa farfado da tattalin arzikin na ta.

Ana iya sauraron sauti daga kasa

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Ediat : Umaru Aliyu