1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin rashin sanin tabbas a Sudan ta Kudu

December 20, 2013

A wannan makon jaridun na Jamus sun fi mayar da hankali ne a kan rikice-rikice a kasashen Sudan ta Kudu da kuma Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

https://p.dw.com/p/1Adwy
Hoto: Reuters

A labarinta mai taken sabuwar kasar Sudan ta Kudu na fuskantar barazanar fadawa cikin wani yakin basasa, jaridar Süddeutsche Zeitung cewa ta yi.

"Shekaru biyu da rabi ke nan da kirkiro sabuwar kasar. Lokacin bikin 'yancinta, 'yan kasar sun yi shagulgula da yin addu'o'i na sabuwar walwalar 'yanci daga Sudan ta Arewa da suka shafe shekaru gommai suna yakin basasa. Sai dai fatan samun zaman lafiya mai dorewa ya gushe a kwanakin bayan nan inda yanzu sabuwar kasar kanta ke fuskantar barazanar tsunduma cikin wani yakin basasa. Wannan ya faro ne bayan harbe-harbe da aka yi a kusa da fadar shugaban kasa dake Juba babban birnin kasar a ranar Lahadi da ta gabata, abin da shugaba Salva Kiir ya alakanta da wani yunkurin juyin mulki daga mataimakinsa Riek Maschar. Tun dai a cikin watan Yuli gwagwarmayar neman rike madafun iko tsakanin mutane biyu ta yi tsanani. Ba da wata-wata ba shugaba Kiir ya kori Maschar wanda tun da dadewa yake sha'awar zama shugaban kasa."

Rashin jin gajiyar arzikin man fetir

Jaridar ta ci gaba da cewa, har yanzu kasar ta Sudan ta Kudu ba ta ci moriyar sabon 'yancin da ta samu ba. Aikin hakar manta ba ya tafiya yadda ya kamata saboda takaddamar tsakaninta da Sudan ta Arewa, inda bututun man suka ratsa. Sannan akwai rashin jituwa tsakanin kabilun kasar. A dangane da rikice-rikice ana saka ayar tambaya game da makomar kasar."

Südsudan Süd Sudan Flüchtlinge Unruhen Juba
Hoto: Reuters

Gwagwaryamar rike madafun iko a Sudan ta Kudu inji jaridar Der Tagesspiegel tana mai cewa shugaba Kiir ya yi zargin yunkurin juyin mulki amma tsohon mataimakinsa ya musanta yayin da daruruwan mutane suka rasu sakamakon rikicin kasar.

"Gwagwarmayar neman rike madafun iko a Sudan ta Kudu tsakanin shugaba Salva Kiir da tsohon mataimakinsa Riek Maschar ta rikide zuwa wani rikici. Ko da yake a ranar Laraba kura ta lafa a birnin Juba, amma an kiyasce cewa mutane kimanin 500 suka rasa rayukansu sakamakon rikicin da aka fara tun ranar Lahadi sannan wasu dubu 20 sun nemi mafaka a harabar dakarun Majalisar Dinkin Duniya dake Juba. Kasar wadda ta samu 'yancin kai a cikin watan Yulin shekarar 2011 ta yi fama da yakin basasa na sama da shekaru 20 da Sudan, sannan ta yi zaman wucin gadi na shekaru biyar karkashin yarjejeniyar zaman lafiya da Sudan. Sai dai babu hannun gwamnatin Khartoum cikin sabon rikicin na Sudan ta Kudu."

Konflikt zwischen Christen und Muslimen in Zentralafrikanischer Republik 10.12.2013
Hoto: picture-alliance/dpa

Mawuyacin hali a birnin Bangui da kewaye

A kowace rana dubban mutane ake kora daga yankunansu inji jaridar Die Tageszeitung tana mai mayar da hankali a kan halin da ake ciki a Bangui babban birnin Jamhuriyar Afirka ta tsakiya, inda mutane ke neman tsira daga ayyukan sojojin sa kai. Jaridar ta ce yanzu haka mutane fiye da dubu 210 suka tsere sai dai 'yan kalilan ne dagha cikinsu ke samun wata kulawa ta a zo a gani. Wasu hotuna da aka dauka ta kumbon satelite sun nuna yadda dubban mutane ke kwarara wasunsu zuwa filin jirgin saman Bangui inda aka kakkafa tantuna, wasu kuma cikin daji wasu kuma bisa addinin da suke bi, sun nemi mafaka a cikin masallatai da gine-ginen coci."

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman