1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin rashin sanin tabbas a Turai bayan zaben Italiya

February 27, 2013

Sakamakon zaben Italiya, ya jefa siyasar kasar cikin halin rashin tabbatas, wanda ke janyo tsoro kan makomar kasar musamman ta fannin tattalin arziki.

https://p.dw.com/p/17n1Y
Electoral placards showing Democratic Party (PD) leader Pier Luigi Bersani (L) and right-wing Silvio Berlusconi are displayed on a wall in Rome on February 26, 2013. Italy was at an impasse Tuesday after an election seen as crucial for the eurozone failed to produce a clear winner and provided a shock debut for a populist anti-austerity party, rattling world markets and setting off alarm bells across Europe. AFP PHOTO / GABRIEL BOUYS (Photo credit should read GABRIEL BOUYS/AFP/Getty Images)
Hoto: AFP/Getty Images

Kasar ta Italiya wadda ke fuskantar komawar tattalin arziki, ita ce kasa ta uku wajen karfin tattalin arzikin tsakanin kasashen Turai. Tun shekara ta 2012 kawo wannan lokaci tattalin arzikin ke ja-da baya. Yanzu kasar tana fama da karuwan marasa aiki, inda ko wani daya cikin uku na matasan kasar ke zaman kashe wando. Tambayan da 'yan kasar ke yi ita ce, shin ina matakan tada komadan tattalin arzikin da Firaminista Mario Monti ya dauka. Wannan hali shi ne 'yan siyasa masu nuna adawa da shiga gamayyar kudin Euro ke amfani da shi, wanda ya janyo tsohon firaminista Silvio Berlusconi da tsohon dan wasan barkwanci Beppe Grillo samun rabin kuri'un da aka kada.

Nicolas Heinen masanin tattalin arziki a babban bankin Jamus na Deutsche Bank:

"Rashin aiki ya yi katutu musamman tsakanin matasa. Amma wannan ba sakamakon matakan tada komadan tattalin arziki ba ne, saidai soboda kwashe shekaru ba a dauki matakan da su ka dace a dauka ba, abun da ya janyo wadanda su ke aiki su ka ci gaba, barasa aiki kuma ta su ka rasa nayi."

Duk da shekarun da aka kwashe cikin wannan hali. Mario Monti ya yi kokarin gudanar da sauye sauyen tada komadan tattalin arziki. A matsayinsa na farfesa kan tattalin arziki wanda ya shafe shekaru a kasashen ketere, ya yi amfani da kwarewa kan harkokin tattalin arzikin kasar. Akwai masu suka wadanda su ka nuna rashin gamsuwa da matakan ta fannin siyasa, Andreas Freytag farfesa kan tattalin arziki a Jami'ar Jena:

Electoral posters are seen in Rome February 26, 2013. The Italian stock market fell and state borrowing costs rose on Tuesday as investors took fright at political deadlock after a stunning election that saw a protest party lead the poll and no group had a clear majority in parliament. REUTERS/Max Rossi (ITALY - Tags: POLITICS ELECTIONS)
Hoto: Reuters

"Wannan tsari ne na neman riba, wanda ke mayar da tsarin tada komada sahun baya, tare da duba sauran bangarori, wanda shi yasa ake fuskantar rashin gamsuwa."

Wasu kasashen na gamayyar Turan da rikicin tattalin arzikin ya turnike sun hada da Portugal da Spain.

Masanin tattalin arziki Nicolas Heinen ya kawar da yuwuwar bazuwar wannan matsala ta tattalin arziki zuwa wasu kasashen:

"Gaskiya ita ce, yanayin da ake ciki a kasashen Turai kan hanun jari ba kamar na shekara ta 2010 da 2011, yanzu muna da shiri na Babban Bankin Turai, wanda dukufa domin ceto kudin Euro ta ko wani hali."

Jagoran masu ra'ayin gabadai-gabadai na kasar Italiya Pier Luigi Bersani ya tabbatar da kalubalen da ke gabansa, duk da samu matsayi na farko, ba yi da rinjayen da zai kafa gwamnati.

Bersani ya ce, kuri'ar adawa da shirin tsuke bakin aljihu da 'yan kasar su ka kada, wannan ya janyo rudani kafa gwamnati cikin majalisar dokoki.

Gamayyar jam'iyyu masu ra'ayin gabadai-gabadai da Luigi Bersani ya jagoranta ta samu rinjae amma bai kai na kafa gwamnati kai tsaye ba, yayin da masu ra'ayin mazan jiya na tsohon Firaminista Silvio Berlusconi ke matsayi na biyu.

A TV screen showing news on Italy's former Prime Minister Silvio Berlusconi is pictured in front of the German share price index DAX board at the German stock exchange in Frankfurt February 26, 2013. REUTERS/Lisi Niesner (GERMANY - Tags: BUSINESS POLITICS)
Hoto: Reuters

Bisa tsarin mulkin kasar ta Italiya majaliasa za ta fara zama cikin kwanaki 20 da gudanar da zabe, sannan a fara tattaunawa kan kafa gwamnati tare da Shugaba Giorgio Napolitano. Tuni kasashen Turai su ka fara mayar da martani bisa zaben na Italiya, inda su ke neman ganin kafa gwamnati wadda za ta ci gaba da manufofin tsuke bakin aljihu, domin ceto tattalin arzikin kasar daga shiga rudani.

Mawallafa: Danhong Zhang / Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal