1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin rashin tabbas a birnin Kunduz na arewacin Afghanistan

Bernd Riegert/SBSeptember 30, 2015

Mamaye birnin Kunduz da Taliban ta yi ya nuna bukatar kasancewar NATO a kasar lokaci mai tsawo fiye da yadda aka tsara.

https://p.dw.com/p/1Gg8d
Afghanistan Kämpfe um Kundus
Hoto: Getty Images/AFP

Kungiyar tsaro ta NATO ta nuna takaicin faduwar birnin Kunduz da ke arewacin kasar Afghanista a hannun tsagerun Taliban, inda ake ci gaba da fafatawa domin sake mayar da birnin karkashin ikon dakarun gwamnati.

Kungiyar tsaron ta NATO ko OTAN ta tabbatar da cewa dakarunta na musamman gami da na Amirka sun kaddamar da sabbin hare-hare ta sama kan mayakan kungiyar Taliban da suka samu nasarar shiga birnin Kunduz a farkon mako. Rahotanni sun tabbatar da cewa 'yan kungiyar Taliban sun tsere daga wasu wurare bayan musanyar wuta na tsawon lokaci, kuma dakarun gwamnatin Afghanistan na ci gaba da rike filin jirgin sama na birnin.

Afghanistan Taliban Kämpfer in Kundus
Mayakan Taliban bayan sun kwace birnin KunduzHoto: Getty Images/AFP

Mohammed Qasim Jangalbagh babban jami'in 'yan sanda na birnin Kunduz ya ce suna samun nasara sosai kan mayakan Taliban.

"Yanayin yana inganta, jami'an tsaro sun sake kwato wasu wurare, kuma ana ci gaba da fafatawa. Mun sake kwace sabuwar shalkwatar 'yan sanda da gidan fursuna da wasu bangarori na birnin. Muna sake mamaye birnin."

Zaman dar-dar da rashin tabbas

Babu wani cikakken labari kan abin da ke faruwa a cikin birnin inda mutane suke zaman tsaro da rashin tabbas kan abin da zai iya faruwa da su. Rahotanni sun tabbatar da cewa dakarun kundunbala na musamman na kasashen ketare sun shiga fafatawa da Taliban.

Shekaru 14 bayan kawo karshen gwamnatin Taliban kana shekara guda bayan Shugaba Ashraf Ghani ya dauki madafun iko, sai gashi dakarun kasar ta Afghanistan duk da makudan kudaden da aka kashe na horas da su, sun gaza rike daya daga cikin birane masu muhimmanci na kasar. Roland Freudenstein masanin harkokin tsaro ya ce mahukuntan birnin Kabul suna da sauran aiki:

"Babu wani abu na rashin jin dadi game da kamun ludayen Shugaba Ashraf Ghani da ya cika shekara guda kan madafun iko. A fannin soji za a iya cewa sojojin Afghanistan ba su da muhimmin tasiri da ya wuce birnin Kabul. Ba abu ne da zai faru a nan kusa ba."

Masanin harkokin tsaron na ganin 'yan Taliban da suke yankin kudanci za su samu karfin gwiwa.

Kuskure ne janye sojojin ketare

Afghanistan Ursula von der Leyen vor einem Hubschrauber
Ministar tsaron Jamus Ursula von der LeyenHoto: picture-alliance/dpa/T. Peter

Ursula von der Leyen ministar tsaron Jamus ta nuna adawa da janye sojojin Jamus baki daya saboda irin tashin hankali da zai iya faruwa.

"Mu tare muka shiga da sauran kawayenmu kuma tare za mu janye. Wannan haka yake. Duk ba mu yi haka domin jefa nasarar da muka samu cikin hadari ba. Abubuwa da suke faruwa cikin yankin sun nuna muhimmancin rashin ficewa daga kasar wadda take tangal-tangal wajen gina kanta musamman kan samar da tsaro."

Birnin na Kunduz yana dauke da mazauna kimanin dubu 300 kuma ya kasance birnin mafi girma da mayakan Taliban suka kwace tun shekara ta 2001, kimanin shekaru 14 da suka gabata, bayan kawo karshen gwamnatin kungiyar, karkashin jagoranci kutsen da Amirka ta yi.