1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hana saka matasa aikin tarzoma a Faransa

Ahmed SalisuDecember 15, 2014

Rundunar 'yan sandan Faransa ta ce ta tarwatsa masu dauka tare da tura matasa kasar Siriya don gudanar da jihadi tare da masu kaifin kishin addini a kasar.

https://p.dw.com/p/1E4Ev
Al-Kuds Berlin Anti-Israel Demonstration Palästinenser 25.07.2014
Hoto: picture-alliance/dpa

Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ce da sanyin safiyar Litinin din nan ce 'yan sandan suka afka wa wurare da dama a fadin kasar musamman ma birnin Paris da Toulouse da kuma Normandy.

Ya zuwa yanzu dai ba a yi karin haske ba game da adadin wadanda aka kama sakamakon sumamen. Da ma dai jami'an tsaro da ma hukumomin Faransa sun jima suna nuna fargabarsu dangane da yadda suka ce matasa a kasar na shiga ayyuka na tarzoma.