1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hanyoyin inganta ma'amala tsakanin Jamus da Masar

January 30, 2013

Mohammad Mursi ya ziyarci Jamus a daidai lokacin da ƙasar Masar ta faɗa cikin mawuyacin halin tattalin arziki da rikicin siyasa.

https://p.dw.com/p/17U4w
Berlin/ Bundeskanzlerin Angela Merkel (CDU) und der aegyptische Praesident Mohammed Mursi geben sich am Mittwoch (30.01.13) im Bundeskanzleramt in Berlin die Hand. Merkel und Mursi trafen sich, um ueber die innenpolitische Lage in Aegypten zu sprechen. (zu dapd-Text) Foto: Axel Schmidt/dapd
Merkel und Mursi in Berlin PK 30.01.2013Hoto: dapd

A wannan Laraba shugaban ƙasar Masar Mohammad Mursi zai kawo ziyara farko a ƙasar Jamus tun bayan da ya hau shugabacin ƙasar a shekara da ta gabata.

Saidai wannan ziyara za ta wakana a daidai lokacin da Masar ta shiga wani halin tashe-tashen hankula.

Kasar Masar ta cika shekaru biyu da ƙaddamar da juyin juya hali, wanda ya kifar da mulkin tsofan shugaban ƙasa Hosni Moubarak, to saidai bikin cikar shekarun biyu ya wakana cikin yanayin rikici, wanda ya haddasa mutuwar mutane da dama.

Shugaba Mohammad Mursi, ya shiga wani hali na gaba kura bayan sayaki tsakanain 'yan adawa da kafofin sadarwa masu matsa masa lamba.A fitowarta ta makon da ya gabata, jaridar Al Masry al Yaum ta yi sharhi da cewar al'uma na buƙatar cenji, kamar dai yadda duban jama'a ke cigaba da faɗa a dandalin Tahrir.

A ziyarar da zai yi a wasu ƙasashen Turai Mohammad Mursi zai tattana da takwarorinsa game da halin da ƙasarsa ke ciki.

Egyptian protesters stand on a police vehicle before they set it on fire in Cairo's Tahrir Square on January 28, 2013. Egypt's main opposition bloc rejected an invitation by President Mohamed Morsi for talks on the violence and political turmoil sweeping the country and instead called for fresh mass demonstrations. AFP PHOTO / MAHMOUD KHALED (Photo credit should read MAHMOUD kHALED/AFP/Getty Images)
Hoto: Getty Images

A cewar Rupchert Polenz na jam'iyar CDU, bugu da ƙari shugaban komitin kula da harkokin ƙetare a Majalisar Dokokin Bundestag ya zama wajibi Mursi ya yi bayani game da alƙiblar da ya sa gaba, hasali ta fannin rikicin siyasar da ya ƙi yaƙi cenyewa a ƙasar ta Masar:

Yace:Abun baƙin ciki ne,ganin yadda 'yan siyasar Masar su ka kasa cimma daidaito game da saban kundin tsarin mulki,sannan abin takaici ne gannin yadda shugaba Mursi ya yi gabansa gaɗai ta fannin ƙaddamar da saban kudin, ba tare da cimma yarjejeniya ba da ɓangarori daban daban na ƙasa.Wannan mataki idan ba a yi taka tsatsan ba, zai mayar da hannun agogo baya, a yunƙurin samar da murmurewar ƙasar daga martsalolin da ta yi fama da su.

Wani daga mahimman batutuwa da ɓangarorin biyu za su mai da hankali akai, albarkacin wannan ziyara shi ne batun riƙidar Masar zuwa wata ƙasa mai mulkin tare da yin dogaro da shari'ar musulunci, matakin da wasu 'yan ƙasar ke dangatawa da tauye haƙƙin mabiya sauran addinai, kamar yadda Klaus Brandner na jam'iyar SPD, kuma shugaban komitin ma'amala tsakanin Jamus da Masar a Majalisar dokokin Bundestag ya yi baiyani:

Ya ce: Ta kamata shugaba Mohammad Mursi yayi la'akari da haƙƙoƙin dukan ɓangarori al'umar Masar.Nuna fifiko ga wani addini ba zai haifarawa ƙasar ɗa mai ido ba.Idan da so samu ne, ya ɗauki misali da ƙasar Turkiyya, inda hukumomin wannan ƙasa ke iya ƙoƙarinsu, domin bunƙasa tattalin arzikin da kyautata rayuwar jama'a tare da assasa cude ni in cuɗe ka tsakanin mabiya addinai daban-daban.

Wani batu da ke ciwa Jamus tuwa a ƙwarya game da ma'amalarta da Masar shine matsalolin da Gidauniyar Konrad Adenauer ke cin karo su a ƙasar wajen gudanar da aiyukanta ,wanda shima a cewar Rupchert Polenz ta kamata a daddale wannan batu, albarkacin ziyarar Mursi:

BERLIN, GERMANY - JANUARY 30: Protesters demonstrate near the Chancellery prior to the arrival of Egyptian President Mohamed Mursi at the Chancellery on January 30, 2013 in Berlin, Germany. Mursi has come to Berlin despite the ongoing violent protests in recent days in cities across Egypt that have left at least 50 people dead. Mursi is in Berlin to seek both political and financial support from Germany. (Photo by Sean Gallup/Getty Images)
'Yan asulin Masar a Berlin sun yi zanga-zanga lokacin zuwan MursiHoto: Getty Images

"Gidauniyar Konrad Adenauer na fuskantar tsangwama a ƙasar Masar.Ta kamata mu ji daga Mursi, wane shiri yayi, na kare aiyukan ƙungiyoyi masu zaman kansu".

A ɗaya hannun Jamus ta yi amfani da wannan dama, domin jaddada kira ga shugaban ƙasar Masar game da batun kare haƙƙoƙin ɗiya mata, a wannan ƙasa wadda ke cikin mulkin ƙungiyar 'yan uwa musulmi.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi.
Edita: Umaru Aliyu

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani