1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Har yanzu babu mafita ga rikicin Masar

August 5, 2013

Duk da kokarin shiga tsakani a rikicin ƙasar Masar, amma ko wane ya cije kan matsayinsa

https://p.dw.com/p/18Wxl
epa03811057 Supporters of ousted President Mohamed Morsi protest near Rabaa Adawiya mosque after Friday prayer in Cairo, Egypt, 02 August 2013. Egyptian police on 01 August called on backers of ousted Islamist president Mohammed Morsi to end sit-ins in two Cairo areas signalling an imminent security crackdown upon the large protests.The Interior Ministry which is in charge of security forces said it had started taking necessary measures to end the vigils in the area of Rabaa al-Adawiya in eastern Cairo and al-Nahda Square south of the capital EPA/KHALED ELFIQI
Magoya bayan MursiHoto: picture-alliance/dpa

Duk da fadi tashin ga gamayyar kasa da kasa ke yi domin warware rikicin kasar Masar har yanzu babu alamun cimma tudun dafawa. A wani mataki mai kama da "mai abu ya rantse mara abu ya rantse" bangarori biyu masu gaba da juna a Masar, ko wane bangare ya cije kan matsayinsa. Magoya bayan hamhararren shugaban kasa Mohamed Mursi sun yi alwashin ba za su daina zanga-zanga ba, sai ya koma kan karagar mulki, a yayin da su kuwa sojojin da suka kwace ragamar mulki su ka ci gaba da yin kunnen uwar shegu game da wannan bukata.
Masu zanga-zanga sun yi burus da gargadin da sojojin su ka yi musu na ficewa daga wuraren da suka yi zaman durshi. Rahotani daga birnin Alkahira, sun tabbatar da cewar a wanan Litinin wata tawagar masu shiga tsakanin daga kasashen ketare ta gana da shugabanin kungiyar 'yan uwa musulmi da ke tsare a kurkuku.Tawagar da ta kunshi wakilai daga Amirka, Kungiyar Tarayyar Turai da kasashen larabawa, ta gana da Mohammed Badie da Chairat al-Chater, wanda sabbin hukumomin Masar ke zargi da hannu a tashin hankalin da ya barke a kasar, tun bayan kifar da shugaba Mohammad Musri a watan da ya gabata.
Sai dai tunanin Günter Meyer na cibiyar nazarin siyasa da zamantakewa a kasashen Larabawa dake jami'ar Mainz a kasar Jamus, abin da kamar wuya a gano bakin zaren wannan takkaddamar:
"Yunkurin warware wannan rikici ta hanyar diplomasiyya na cin karo da babban tarnaki. Bangarorin biyu ko wane ya yi tsayuwar gwamen jaki game da manufofinsa."
To saidai duk da cijewar da al'amuran su ka yi a fadi tashin shawo kan rikicin na kasar Masa,r ba za yanke kauna ba inji Meyer kuma ya ba da hujjoji:
"Demokradiyya tsarin mulkin ne mai wahalar gikuwa, ba wai don an kifar da mulkin kama karya ba ne kawai, sai demokradiyya ta samu. Sannu a hankali da rarrafe yaro ke tashi. A nan kasashen Turai, hasali ma Jamus, sai da aka share shekaru masu yawa, kamin demokradiyya ta zauna da gindinta, na yi imanin Masar ma za ta samu cikkakar demokradiyya".
A yayin da gamayyar kasa da kasa ke kokarin samun masalaha a cikin wannan rikici, sojojin dake mulkin a Masar sun baiyana ranar 25 ga watan da muke ciki domin gurfanar da shugabanin kungiyar 'yan uwa musulmi biyu da ake zargi da hannun a cikin rikicin. Duk da cewar sanarwa ta mayar da hannun agogo baya, amma fa ba a yanke kauna inji Hamadi El-Aouni masanin kimiyyar siyasa a jamai'ar birnin Berlin:
"Nan da watani uku zuwa shida na tabbatar da za a kawo karshen rikicin kasar Masar, komi zai tafi daidai."
Hausawa kan cewa wai fata na gari lamiri, kamin nan dai har yanzu dubun dubunan membobin kungiyar 'yan uwa musulmi sun sadaukar da rayuka domin cimma burin da suka sa gaba.
Mawallafa: Marcus Lütticke/ Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Usman Shehu Usman

Supporters of deposed Egyptian President Mohamed Mursi sit near tents in their sit-in area around Raba' al-Adawya mosque, east of Cairo, August 3, 2013. Egypt's army-backed rulers and allies of its deposed Islamist president gave the first signs on Saturday of a readiness to compromise, pressed by Western envoys trying to head off more bloodshed. REUTERS/Asmaa Waguih (EGYPT - Tags: POLITICS CIVIL UNREST)
Magoya bayan Mursi, cikin sansanin da suka kafaHoto: Reuters
Supporters of first democratically elected president Mohamed Morsi move towards the Republican Guard Headquarters to protest military coup held in the country. Cairo, Egypt, on July 19, 2013. Photo by Ahmed Ismail/AA/ABACAPRESS. COM
Sojojin Masar cikin shirin ko-ta-kwanaHoto: picture alliance / abaca
epa03812017 A handout photo released and taken by the Egyptian Presidency on 03 August 2013 shows US Deputy Secretary of State William Burns (L) meet with Egyptian Vice President Mohamed El-Baradei (R) in Cairo, Egypt. Burns is on a visit to Egypt to hold talks about finding a peaceful solution to the recent protests held in support of ousted president Mohamed Morsi. EPA/EGYPTIAN PRESIDENCY / HANDOUT MANDATORY CREDIT: EGYPTIAN PRESIDENCY HANDOUT EDITORIAL USE ONLY/NO SALES
William Burns manzon da Amirka ta tura a rikicin Masar, tare da El Baradei, mataimakin shugaban kasar Masar.Hoto: picture-alliance/dpa
Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani