1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Haramcin gangamin zabe a Kinshasa

Yusuf Bala Nayaya
December 19, 2018

Kwanaki kafin babban zabe a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango mahukuntan birnin Kinshasa sun haramta yakin neman zabe a babban birnin kasar saboda dalilai.

https://p.dw.com/p/3AP28
DR Kongo Wahlkampf in Kinshasa
Hoto: Getty Images/AFP/J.D. Kannah

Gwamnan birnin na Kinshasa Andre Kimbuta ya bayyana a wannan rana ta Laraba cewa an haramta gangamin yakin neman zaben ga 'yan takara 21 wadanda ke neman shugabancin kasar ta Kwango a zaben da za a yi a ranar 23 ga watan Disamba. Wannan umarni dai ya sanya dan takarar shugabancin kasar daga bangaren adawa Martin Fayulu ya fasa gangamin zabensa da ya tsara yi a wannan Laraba, ko da yake magoya bayan dan takarar sun taru a gefen tituna suna dakon na Fayulu sai dai sun share sa'oi ba tare da ya bayyana ba.

Gwamnan na Kinshasa Kimbuta ya bayyana cewa sun samu bayanai da ke nuni da cewa akwai wasu masu tsatstsauran ra'ayi da suka tsara za su kai hare-hare a kwanakin karshe na yakin neman zabe don haka, dalilai na tsaro ya sa suka dau matakin.