1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare-hare a Iraƙi ya hallaka mutane da dama

March 19, 2013

Wasu hare-hare a Iraƙi sun hallaka mutane 50 mutane da dama kuma sun jikkata, gabanin cika shekaru 10 da mamayar da Amirka ta yi wa ƙasar

https://p.dw.com/p/180CR
Residents gather at the site of a car bomb attack in the AL-Mashtal district in Baghdad March 19, 2013. A series of coordinated car bombs and blasts hit Shi'ite districts across Baghdad and south of the Iraqi capital on Tuesday, killing at least 25 people on the tenth anniversary of the U.S.-led invasion. REUTERS/Mohammed Ameen (IRAQ – Tags - Tags: CONFLICT CIVIL UNREST TPX IMAGES OF THE DAY)
Hoto: Reuters

A yayin da ake jajibirin bukin cika shekaru goma da mamayar da Amurka ta yi wa Iraƙi, wasu hare-hare sun kai ga hallakar mutane aƙalla 50, haka nan kuma hukumomi sun jinkirta gudanar da zaɓukkan gundumomi suna bada hujjar matsalolin tsaro.

Fashewar wasu abubuwa 20 da kisan gilla biyu sun bar aƙalla mutane 170 da rauni, a wani yanayin da ya fi kawanne baƙin ciki a tsakanin watanni shiddan da suka gabata, abun da kuma ke nuna irin tashe-tashen hankula, da rikicin siyasar da yunƙurin Amirka na samun abokiyar ƙawance ta demokraɗɗiya a Yankin Gabas ta Tsakiya ya janyo.Yawancin hare-haren sun afku ne a unguwannin 'yan shi'an da ke birnin Bagadaza.

Babu dai ƙungiyar da ta ɗauki alhakin wanna hari.To sai dai Kamfanin dillancin labarai na Faransa, ya rawaito cewa gabannin bukin na cika shekaru 10 mutane 114 suka hallaka tun daga makon da ya gabata. ko da shike hukumomin basu bayyana ko za'a a gudanar da wani taro na tuna wannan rana ba sai dai wata ƙila za'a tuna da faɗuwar birnin Bagadaza a ranar tara ga watan Afrilu idan Allah ya kai mu.

Mawallafiya: Pinado Abdu Waba
Edita: Usman Shehu Usman