1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AQIM na kai harin ta'addanci a Afirka

Umaru Aliyu / LMJMarch 14, 2016

Kungiyar tarzoma da aka sani da suna AQMI ko AQIM, ita ce ta baya-bayan nan cikin kungiyoyin 'yan tarzoma masu tsattsauran ra'ayi da suka yi kaka-gida a yankin Arewacin Afirka.

https://p.dw.com/p/1ICyh
Tutocin kungiyar 'yan ta'adda a Mali
Tutocin kungiyar 'yan ta'adda a MaliHoto: Reuters

Tun a shekaru na 1980 irin wadannan kungiyoyi suke tafiyar da aiyukansu na tarzoma a yankin. Kungiyar AQMI ta samo asalinta ne tun a shekara ta 1997, lokacin da ta rikide daga kungiyar Salafiyya mai gwagwarmayar tabbatar da shari'ar Musulunci a Aljeriya, ko kuma GSPC a takaice, ta koma kungiyar AQIM ko kuma AQMI. Tun a wannan lokaci aka ga alamun cewar kungiyar ta bullo da wani tsari na hadin giwa na kasa baki daya wanda burinsa shi ne shimfida kasa mai bin tafarkin shari'ar Musulunci a yankin Maghreb baki daya, bayan kawar da gwamnatin yankin masu adawa da Musuluncin.

Harin ta'addanci a birnin Abidjan
Harin ta'addanci a birnin AbidjanHoto: Reuters/J. Penney

Ko da yake jami'an tsaron Aljeriya sun sami nasarar kawar da barazanar mayakan na kungiyar AQMI amma ba'a ci karfinsu gaba daya ba, inda a maimakon haka suka janye zuwa Arewacin Mali, domin kafa sabon tushe na hadin gwiwa a tare da kungiyoyi a yankin. Masani kan harkokin tsaro William Assanvo ya ce ko da ya ke kungiyar AQIM ta na da rassanta da dama, amma reshenta na Arewacin Mali shine ya fi muhimmanci, saboda ya zuwa shekara ta 2012, reshen ya kasance mai rundunoni daban-daban har guda hudu, da ke dauke da daruruwan mayakansa.

Kamal Ben Younes na cibiyar nazarin harkokin tsaron kasashen Afirka da Larabawa da ke Tunis ya ce:

AQIM matsala ce ta kasa da kasa

"Wannan matsala ce da tilas a yi nazarinta a matsayin matsala ta kasa da kasa. Kungiyar AQIM ba a kasa daya take aiyukan ta ba, kuma hare-harenta basu tsaya wuri guda ba. Wannan kungiya da rassanta, suna aiyukansu a kasashe 23 tun daga Afirka ta Arewa har zuwa yankin Maghreb da na Sahara. A wadannan wurare har yanzu akwai makamai masu tarin yawa da sukai asalinsu daga zamanin mulkin Gaddafi na Libiya da suka fada hannun wadannan kungiyoyi da ke yaki da gwamnatoci masu kusantar kasashen yamma. Bayan faduwar gwamnatin Gaddafi da rushewar Libiya mun ga yadda makaman suka fada hannun 'yan tarzoma daga Libiyan zuwa Chadi da Nijar da Mali da Najeriya da Burkina Faso. Kada kuma mu manta da cewar gwamnati a Ouagadougou ta kasance mai kyakkyawar dangantaka da gwamnatin Gaddafi."

Kungiyar AQMI ta na kuma cin gajiyar tuntubar juna da ke tsakaninta da wasu kuingiyoyi na tarzoma kamar Al-Murabitun ko Ansar Dine, wadda kungiya ce ta 'yan ta'aadda ta Buzaye da ta bullo a yankin bayan kayar da gwamnatin Libiya ta Gaddafi. Ko da yake wadannan kungiyoyi sun ban-banta game da akidojinsu da kabilunsu, amma gaba daya burinsu guda ne saboda haka suke hada kai domin cimma wannan buri.

Burkina Faso ma ta fuskanci hari a Janairu
Burkina Faso ma ta fuskanci hari a JanairuHoto: Getty Images/AFP/A. Ouoba

Sabani a kungiyoyin tarzoma

William Assanvo na cibiyar nazarin zaman lafiya da ke Dakar ya ce ko da yake kungiyoyi suna da buri guda, amma suna kuma da ban-banci tsakaninsu a game da wanda zai jagoranci Jihadi a yankin na Arewacin Afirka.

Ya ce: Takarar da ke akwai a yanzu ita ce wacce ce daga cikin kungiyoyin za ta jagoranci jihadi a duniya abaki daya, musmaman ganin cewar a yanzu din kungiyar IS ita ce ake dauka a matsayin jagorancin jihadin. Ita ma kungiyar al-Qaeda tana da hannu a wannan gwagwarmaya a wani yunkuri na farfado da darajarta. Dangane da haka ina ganin muna iya kwatanta hare-haren da aka kai Ouagadougou da Bamako a watan Nuwamba na bara a matsayin wani yunkuri na AQMI domin tabbatar da karfin da take da shi a wannan yanki."