1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hari a fadar shugaban kasar Somaliya

July 8, 2014

Kungiyar al-shabbab ta kai hari a fadar shugaban kasar somaliya da ke Mogadishu ba tare da samun shugaba Hassan Sheikh Mahamud a ciki ba.

https://p.dw.com/p/1CYMh
Hoto: picture alliance/AP Photo

Mayakan Kungiyar al-Shabaab da ke gaggwarmaya da makamai a Somaliya sun yi amfani da bam da kuma bindigogi wajen kai hari a fadar shugaban kasa da ke birnin Mogadishu. Wadanda suka shaidar da lamarin sun bayyanna cewar sun ji harbe-harben rokoki da kuma barin bindigogi a cikin fadar ta shugaban kasa.

Wata majiyar tsaro ta bayyana cewar shugaba Hassan Sheikh Mohamud ba ya cikin fadar lokacin da aka kai wannan harin. Sai dai kuma wani jami'in gwamnati ya nunar da cewa mayakan na al-Shabaab da ke da alaka da Alka'ida sun yi nasarar kutsawa cikin fadar ta shugaban kasa. Yayin da kakakin kungiyar a nasa bangaren Sheikh Abu Musab ya nunar da cewar sun mayar da wasu sassa na fadar karkashin ikonsu.

Wannan dai ba shi ne karon farko da al-Shabaab ke kai hari a kan fadar shugaban kasar Somaliya ba. Ko watanni hudun da suka gabata sai da ta dauki irin wannan mataki, wanda ma ta maimaitashi a majalisar dokoki a watan Mayun 2014. Tun bayan da sojojin kasa da kasa na Amisom suka fatattakesu daga Mogadischo shekaru biyun da suka gabata ne, mayakan al-Shabaab suka canja salon kamun ludayinsu inda suke gudanar da yakin sunkuru tare da kai hare-hare a kan kadarorin gwamnati.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Pinado Abdu-Waba