1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hari a gidan shugaban majalisar Nijar

February 17, 2014

Wasu mutanen da ba'a san ko su waye ba, sun kai hari a gidan shugaban jam'iyyar Lumana Afrika kuma shugaban majalisar dokokin Nijar, Hama Amadou wanda ke ziyara a Iran.

https://p.dw.com/p/1BASf
Niger Anschlag auf Hama Amadou Opposition
Hoto: Mahaman Kanta

Shugaban jamiyyar ta Lumana Afrika reshen birnin Yamai ya ce ba
wanda ya jikkata a cikin wanan hari, amma kuma tuni ya danganta harin da wata makarkasshiyar neman kashe shugaban jam'iyyar tasu da ya ce wasu da bai fadi sunansu ba ke son yi a kasar ta Nijar. Yanzu haka dai jami'an bincike na ci gaba da gudanar da aikin binciken lamarin a gidan Malam Hamma Amadou.

Daruruwan magoyan bayan shugaban jamiyyar Lumana Afrika na kasa baki daya Malam Hamma Amadou ne dai su ka yi cincirindo tun da sanyin safiyar wannan litinin a gaban gidan nasa da ke a unguwar yantalar birnin Yamai domin gane wa idanunsu da ma kawo goyan bayansu ga shugaban nasu.

Da ya ke jawabi a gaban manema labarai a gaban harabar gidan shugaban jam'iyyar tasu Malam Sumana Sanda ya ce da misalin karfe sha biyu da rabi na daren jiya ne lamarin ya auku.

Sai dai duk da kasancewarmu a kofar gidan har ya zuwa lokacin hada wanann rahoto babu wata kafar yada labarai ta radio ko ta talabijin da ta samu izinin shiga gidan domin gane wa idanunta gaskiyar lamarin kasancewa jami'an tsaro masu gudanar da bincike na a ciki suna gudanar da aikinsu a cewar shugaban jam'iyyar na reshen birnin Yamai Malam Sumana Sanda wanda ko da ya ke ya ce kawo yanzu ba su dora alhakin lamarin a kan wani ba amma ya danganta harin da wata makarkashiyar neman hallakar da shugaban jamiyyar tasu.

Wannan lamari ya zo ne a daidai loakcin da batun zargin kabilanci ya mamaye fagen siyasar kasar ta Nijar tsakanin 'yan adawa da bangaran masu milki. A kan wanann batu ne ma dai kawancen wasu kungiyoyin addinin muslunci na kasar Nijar su ne suka fitar da wata sanarwa inda su ka ja hankalin 'yan siyasa dama duk wasu masu rura wutar kywama da kabilanci
a tsakanin 'yan kasar ta Nijar a yau.

Kawo yanzu dai gwamnatin kasar Nijar ba ta kai ga cewa uffan ba a kan wanann lamari sai dai tuni komitin koli na jamiyyar ta Lumana Afrika ya kira wani taron gaggawa a yau da yamma domin yin nazarin wanann lamari dama bayyan matsayinsa akansa.

Niger Anschlag auf Hama Amadou Opposition
Uwargidan Hama Amadou ta na karbar gaisuwaHoto: Mahaman Kanta

Mawallafi: Gazali Abdu Tasawa
Edita : Zainab Mohammed Abubakar