1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane 73 sun halaka a harin Burkina Faso

Zulaiha Abubakar
November 7, 2019

Jama'a da dama sun bace sakamakon wani farmaki da wasu mahara suka kai wa ma'aikata a yankin da kasar Burkina Faso da ake aikin hakar ma'aidinai yayin da mutane 73 sun rasa rayukansu lokacin harin.

https://p.dw.com/p/3SeLS
Mauretanien G5 Sahel Taskforce
Hoto: Getty Images/AFP/T. Samson

Mahara sun kai wa jerin gwano motocin daukar ma'aikatan kamfanin hakar gwal na kasar Kanada mummunan hari a yankin gabashin kasar Burkina Faso al'amarin da ya firgita ma'aikatan da kuma wadanda ke harabar da ibtil'in ya faru. Ita dai kasar Burkina Faso ta zama mafakar masu tsattsauran ra'ayin addinin Islama duk da aikin hadin gwiwar tsaro da hadakar jami'an tsaro kasar suke yi don kawo karshen ta'addanci a fadin kasar da ke Yammacin Afirka.

Mauretanien G5 Sahel Taskforce
Hoto: Getty Images/AFP/T. Samson

Shekaru biyar da suka gabata kasashen yankin Sahel suka kirkiri G5 Sahel da nufin kawo karshen ta'addanci da yaduwar tsattsauran ra'ayin addini tsakanin kasashen yankin da suka hada da kasar ta Burkina Faso. Sai dai har ya zuwa wannan lokaci sojojin Burkina Faso sun fi mayar da hankali a yaki da rikicin da ya addabi kasar har ya fantsama Mali, al'amarin da ya sanya wasu masana ke raina kokarin aikin tsaron hadakar na G5 Sahel.

Shugabannin Yammacin Afirka sun sanar da wani shiri da zai lakume makudan kudade a shekarar badi wanda suka dauki alwashin zai kawo karshen ta'addanci gaba daya, a kan wannan kudiri ma Richard Tiene masanin tsaro kuma 'dan jarida ya bayyana shakku game da sojojin kasar ta Burkina Faso.

Biyo bayan zafafa hare-haren ta'addanci a kasar ta Burkina Faso tun daga shekara ta 2005, sama da mutane 630 ne suka rasa rayukansu sakamakon hare-hare a iyakokin kasar da Mali.