1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al-Shabaab ta kai hari

May 14, 2019

Rundunar 'yan sandan Somalia ta sanar da mutawar kusan mutane goma a sakamakon jerin tagwayen hare-haren bam din da 'yan kungiyar Al-Shabab suka kai a Talatar nan a babban birnin kasar Mogadisho.

https://p.dw.com/p/3IU31
Somalia Autobombe in Mogadischu
Hoto: Reuters/F. Omar

Harin farko ya faru ne a gundumar Warta-Nabadda inda wani dan kunar bakin wake ya tayar da nakiyar da ke jikinsa inda ya kashe mutane shida tare da jikkata wasu 30.

A yayin da nakiya ta biyu ta fashe a lokacin da jerin gwanon tawagar sojin kasar ke sintiri a yankin Afgoye, har sojoji uku suka mutu wasu hudu kuma suka tsira da munanan raunuka, kamar yadda wani jami'in dan sandan Somalia Ali Hassan ya tabbatar.

 Tuni dai kungiyar ta Al-Shabab ta tabbatar da daukar alhakin kai harin ta kafar Rediyonta. Al-Shabab din dai ta kara tsaurara hare-haren ne a cikin wannan wata na Ramadan inda ta ke nufar Otal-Otal da shingen jami'an tsaro da ma gine-ginen gwamnati.