1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Somaliya: Harin al Shabab ya halaka sojoji 27

Ramatu Garba Baba
July 23, 2018

Sojojin Somaliya 27 sun mutu a wani hari da mayakan kungiyar nan ta al Shabaab suka kai kan sansanin sojin Baar Sanguni da ke a kudancin kasar.

https://p.dw.com/p/31tz2
Somalia Mogadischu al-Shabaab Kämpfer
Hoto: picture alliance/AP Photo/M. Sheikh Nor

Rahotanni na nuni da cewa, maharan sun yi anfani da wata karamar mota da suka cika da bama-bamai wajen kai harin na wannan Litinin. Jim kadan da kai harin, kungiyar ta bakin kakakinta Abdiasis Abu Musab ta fitar da sanarwa, inda a ciki ta dauki alhakin kai harin tare da fadin alkaluman sojojin da ta kashe.

Babu bayani daga bangaren hukumomin kasar kan harin da ikirarin kungiyar.  A watan Yunin da ya gabata, mayakan kungiyar sun kai hari a sansanin sojin inda suka raunata sojoji bakwai. Al Shabab na ci gaba da gwagwarmaya da makamai don ganin ta kawar da gwamnatin da ke kan mulki don  kafa ta-ta gwamnati bisa shari'ar addinin Islama.