1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin bam ya kashe mutun 17 a Maiduguri

January 14, 2014

Wani bam da ya fashe a wata kasuwar birnin Maiduguri na Tarayar Najeriya ya haddasa rasuwar mutane 17 kuma da dama sun jikkata

https://p.dw.com/p/1AqYj
Hoto: picture-alliance/dpa

Bam ɗin ya tarwatse ne a tsakiyar 'yan kasuwa masu saye da sayar wa kusa da wani offishin a dai dai lokacin da wata mota cike da itace ke ficewa .Wannan labari ya fito ne daga shugaban 'yan sandar jihar ta Borno Lawan Tanko.

A cewar wani ɗan kasuwar da ya gane wa idanunsa, ya ce wasu da ba'a san ko su wanene ba, suka naɗe bam ɗin cikin wani bahu kuma suka yada shi kusa da masu nama, a kasuwar Jagwal.Shi ma wani da ya gane wa idanunsa, cewa yake nan take ya ga kusan mutun 20 a kwance , sai dai ba shi da tabbacin ko dukka sun mutu. Bam ɗin ya fashe ne a dai dai lokacin da ake yin bukukuwan Maulid

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita: Abdourahamane Hassane