1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin kunar bakin wake ya hallaka wasu dakarun Libiya

March 17, 2014

Akalla Sojoji biyar ne suka mutu, wasu kuma goma suka ji rauni, sakamakon tarwatsewar wata mota shake da bama-bamai kusa da wani barakin sojan Benghazi.

https://p.dw.com/p/1BR35
Anschlag auf Geheimdienst-Offizier in Bengasi
Hoto: Reuters

Akalla dai gawawaki biyar ne aka kai babban asibitin birnin, tare da sauran sassan jikin mutanen da suka tarwatse, da kuma wadanda suka ji rauni sakamakon harin.

A cewar wata majiya ta sojan kasar, motar dai ta kasance a tsaye kusa da barikin, amma kuma ta tarwatse yayin da wani gungun sojoji ke fitowa, daga barikin.

Birnin Benghazi ne dai cibiyar tashe-tashen hankullan da ya haddasa kawar da gwamnatin marigayi Mouammar Kadhafi, inda a halin yanzu wannan birni yake a matsayin wani filin daga, inda ake yawan kai hare-hare ga jamiyan tsaro na yan sanda ko kuma soja.

A ranar 22 ga watan Disamban da ya gabata, harin kunar bakin waken yayi sanadiyar mutuwar wasu jami'an tsaron a nisan km 50 da birnin da Benghazi.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe.