1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin Rasha ya kashe mutane 11 a Ukraine

January 26, 2023

An sami karin mutanen da suka mutu yayin haren-haren da Rasha ta kaddamar a wasu birane na kasar Ukraine, bayan amincewar kasashen Yamma na kara aike wa Ukraine da mayan tankokin yaki.

https://p.dw.com/p/4Ml1B
Wani birnin Ukraine da aka lalataHoto: LIBKOS/AP/dpa/picture alliance

Rahotanni da ke fitowa daga Kiev babban birnin kasar na cewa hare-haren sun halaka akalla mutane 11 da jikkata wasu 11 tare kuma da lalata cibiyoyin samar da lantarki da dama a kasar. A cewar kakakin hukamar aikin agaji ta Ukraine, hare-haren masu matukar muni sun shafi birane 11 na kasar, amma sun fi tsanani ne a kusa da birnin Kiev fadar gwamnatin kasar.

Rasha ta zafafa hare-haren ne bayan amincewar kasashen yamma na kara aikewa Ukraine da mayan tankokin yaki, matakin da fadar Kremlen  ta ce tamkar kasashen sun shiga yakin ne gadan-gadan