1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Sojoji sun halaka a wani hari

Salissou Boukari LMJ
December 12, 2019

A Jamhuriyar Nijar wani hari da 'yan ta'adda suka kai a barikin soja da ke garin Inates mai nisan kilomita 250 da Yamai babban birnin kasar, ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji sama da 70.

https://p.dw.com/p/3Ui6B
Symbolbild- Nigera - Militärübung
Hare-hare kan sojojin Nijar na karuwaHoto: Reuters/A. Ross

Rahotanni sun nunar da cewa 'yan ta'adda sun shiga Jamhuriyar ta Nijar ne daga Mali dauke da manyan bindigogi, inda kuma suka tafka ta'asa a kan sojojin na Nijar. Ofishin ministan tsaron kasar ta Nijar ne ya tabbatar da afkuwar harin tare da adadin wadanda ya rutsa da su. Daga Sanarwar kuma ta ce, an halaka 'yan ta'adda da dama. Koda yake babu wani adadi da sanarwar ta bayar, amma wata majiya da ba ta gwamnati ba ta ce an halaka 'yan ta'addan sama da 50 yayin gumurzun. Da jin wannan labari ne dai na rasura sojojin na Nijar sakamakon harin da 'yan ta'adda daga arewacin kasar Mali suka kai musu a barikin sojojin na Inates, shugaban kasar ta Nijar Issoufou Mahamadou da ke halartar wani babban zaman taro a kasar Masar kan harkokin tsaro da zaman lafiya a Afirka, ya katse bulaguron nashi, inda ya dawo gida Nijar cikin dare kamar yadda gidan talabijin na kasar na Tele Sahel ya bayyana.

Wannan harin wanda shi ne irinsa mafi muni da Nijar ta fuskanta a yankin iyakarta da kasar Mali dai, na zuwa ne a daidai lokalin da al'ummar Jamhuriyar ta Nijar ke tayar da jijiyoyin wuya sakamakon kasancewar sojojin Faransa a kasar, inda ake ganin duk da suna nan bai hana kai muyagun hare-hare ba. Tuni aka shirya gudanar da taron gangami da kungiyoyin fararan hulla suka kira a ranar Lahadi mai zuwa, domin nuna alhini ga hare-haren da sojojin na Nijar ke fuskanta da kuma yadda 'yan Nijar din kamar sauran 'yan uwansu na kasashen Afirka ke kara nuna kyamarsu ga siyasar kasar Faransa a kan kasashen da ta yi wa mulkin mallaka irinsu Nijar din.