1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin ta'addanci a gabacin Afirka

September 27, 2013

Wannan harin ya dawo da aikin tarzoma yankin da shekaru 15 baya wato 1998 kungiyar al-Qaida ta kai mummunan hari a kan ofisoshin jakadancin Amirka dake Kenya da kuma Tanzaniya.

https://p.dw.com/p/19pRQ
A police officer holds a gun to provide cover for customers running out as a shooting took place at Westgate shopping mall in Nairobi September 21, 2013. Kenyan soldiers joined an operation to flush out gunmen who killed at least 15 people in a shopping centre in the capital of Nairobi on Saturday, a Reuters witness said. REUTERS/Noor Khamis (KENYA - Tags: CIVIL UNREST CRIME LAW TPX IMAGES OF THE DAY)
Hoto: Reuters

A wannan makon dai jaridun na Jamus gaba daya sun mayar da hankalinsu ne a kan harin ta'addancin da aka kai a cibiyar kasuwancin nan ta Westgate dake Nairobi babban birnin kasar Kenya.

A labarinta mai taken "Ta'addanci a gabacin Afirka" jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung cewa ta yi kwanaki biyar a jere wata kungiyar 'yan ta'adda daga Somaliya ta jefa duniya cikin tsoro, har zuwa Laraba ranar da aka kubutar da dukkan mutane da suka yi garkuwa kuma aka kawo karshen wannan mummunan lamari bayan kashe mutane da yawa. Jaridar ta ce wannan harin ya dawo da aikin tarzoma zuwa kasar da shekaru 15 baya wato 1998 kungiyar al-Qaida ta kai mummunan harin ta'addancin a Afirka wato ofishin jakadancin Amirka dake birnin Nairobi. Kamar harin na 1998, na wannan makon ma ka iya zama wani sabon babi na ta'addanci. Domin tun abin da ya kama daga yankin tsibirin kasashen Laraba ya zuwa gabacin Afirka, wasu ayyukan tarzoma sun bullo, tare da taimakon kudi daga kasashe irin su Saudiyya ana daukar mayaka daga Yemen da Somaliya. Yanzu al-Shabab ta farfado kuma tana barazana ga kasashe makwabta. Harin na birnin Nairobi ya nuna yadda ta'adda tsakanin 'yan kasahe daban-daban ta dauki wani sabon salo mai hadari."

Foreign forensic experts, flanked by Kenyan military personnel, check the perimeter walls around Westgate shopping mall in Nairobi September 25, 2013. Bomb disposal experts and investigators searched through the wreckage of the Kenyan shopping mall on Wednesday after a four-day attack by Islamist militants that killed at least 72 people. REUTERS/Noor Khamis (KENYA - Tags: CIVIL UNREST MILITARY TPX IMAGES OF THE DAY)--eingestellt von haz
Neman sauran abubuwa masu fashewa a NairobiHoto: Reuters

Ganin laifin juna a Kenya bayan harin ta'addanci

Lokacin sukar lamirin juna a Nairobi inji jaridar Die Tageszeitung tana mai cewa bayan kawo karshen garkuwar da aka yi da mutane a cibiyar kasuwanci ta Westgate ana kara sukar gwamnatin Kenya da hukumomin tsaro da kuma 'yan sanda bisa yin sakaci. Jaridar ta rawaito Sineta Gidion Mbuvi Sonko dake zama abin so ga matasa da talakawan Kenya na cewa tun kimanin watanni biyu da suka gabata ya fada wa hukumar leken asirin kasar game da yiwuwar kai wa kasa ta Kenya hari, bayan wasu mata biyu sun tsegunta masa cewa wasu baki dake gidansu na shirin kai hari. Amma bayan ya kai matan gaban hukumar leken asiri domin karin bayani, shi kenan bai sake jin komai ba. A majalisar dokoki ma ana kara sukar lamirin hukumar da kakkausan lafazi da kuma 'yan sanda da rashin daukar aikinsu da muhimmanci. Sai dai yayin da wannan suka ke karuwa, jaridar ta ce ana ci gaba da bincike a cikin kantunan dake cibiyar kasuwancin ta Westgate don gano abubuwa masu fashewa da karin gawawwaki.

Taylor zai yi sauran rayuwarsa a kurkuku

Daga harin na Kenya sai kuma na laifin yaki. A sharhinta mai taken daurin shekaru 50 ga Charles Taylor, jaridar Süddeutsche Zeitung ta mayar da hankali ga hukuncin da kotun ICC ta tabbatar bayan karar da tsohon shugaban na Laberiya ya daukaka inda ya kalubalancin hukuncin da kotun hukunta laifukan yaki ta duniya dake birnin The Hague ta yanke masa tun farko. Jaridar ta ce yanzu dai tabbatar da wannan hukunci na zama wani abin tarihi ga shari'a ta kasa da kasa, domin hukuncin shi ne na farko da wata kotun hukunta laifukan yaki ta ma wani tsohon shugaban kasa tun bayan shari'ar nan ta birnin Nüremberg bayan yakin duniya ba biyu. An dai samu Taylor da laifin angiza yakin basasan makwabciyar kasarsa Saliyo lokacin da yake rike da mukamin shugaban kasar Laberiya.

** FILE ** Former Liberian President Charles Taylor makes his first appearance at the Special Court in Freetown, in this April 3, 2006 file photo. Taylor's lawyers need more time to prepare his defense against charges he directed a campaign of murder, rape and enslavement in West Africa, his lawyer told a judge Friday Jan. 26, 2007. (AP Photo/George Osodi, Pool, File)
Charles Taylor ya fadi a karar da ya daukakaHoto: dapd

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman