1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saudiya ta fuskanci hare-hare

Lateefa Mustapha Ja'afarJuly 4, 2016

A kalla mutane uku ne suka hallaka sakamakon harin ta'addanci a birnin Madina a wajen Masallacin Masjid al-Nabawi na Annabi Muhammad (SAAW).

https://p.dw.com/p/1JJ0t
Harin ta'addanci a masallacin Masjid al-Nabawi na Madina
Harin ta'addanci a masallacin Masjid al-Nabawi na MadinaHoto: picture alliance/AA/O. Bilgin

Gidan talabijin din Saudiyan na al-Arabiya ya ruwaito cewa, kawo yanzu mutane uku da suka hadar da dan kunar bakin waken da kuma jami'an tsaro biyu sun hallaka. Wannan dai shi ne hari na uku da aka kai a Saudiyan a wannan Litinin din, inda da sanyin safiya wani dan kunar bakin wake ya tarwatsa kansa a wajen ofishin jakadancin Amirka tare da hallaka kansa da kuma jikkata wasu jami'an tsaro biyu, hari na biyu kuwa an kai shi ne a wajen masallacin birnin Qatif na Muslmi mabiya Shi'a, sai dai maharin ne kawai ya hallaka kuma babu wanda ya samu koda kwarzane.