1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harkokin kasuwanci da cinikayya maras shinge a Afirka

Mohammad Nasiru Awal
May 25, 2018

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung wadda ta duba harkokin kasuwanci a Afirka musamman dangane da samar da wani yanki maras shingen ciniki a nahiyar ta ce yana da bukatar karin tabbaci.

https://p.dw.com/p/2yJH2
Symbolbild Afrika Markt Bunt
Hoto: P. U. Ekpei/AFP/Getty Images

Jaridar ta ce kamfanonin Jamus na sahun baya a jerin kamfanonin duniya da ke da hannun jari kai tsaye a kasashen nahiyar Afirka. Dalili shi ne rashin tabbas na dokoki da yawan dogon turanci na hukumomi da kuma uwa uba matsalar cin hanci da rashawa. Sai dai a shekarun bayan nan da yawa daga cikin kasashen Afirka sun inganta dokokinsu da suka shafi batun zuba jari kai tsaye daga kamfanonin ketare.

Sai dai duk wadannan matakai ba su sa an samu karin yawan kamfanonin Jamus da ke fadada harkokinsu a Afirka ba. Amma yarjejeniyar samar da yankin ciniki maras shinge da gomman kasashen Afirka suka rattaba wa hannu a karshen watan Maris na zama matakin farko da zai kawo sauyi mai ma'ana.

Dossierbild 2 Gewalt in Nigeria
Hoto: Reuters

Alhini da takaici a Najeriya inji jaridar Die Tageszeitung,  ta ce bayan wani kisan gilla cocin Ktholika ya kira wani gangami wanda ya samu karbuwa.

Jaridar ta ce cocin Katholika a Najeriya ya yi nasara a inda kungiyoyin kare hakkin dan Adam da sauran kungiyoyi suka gaza duk da kokarin da suka yi. Ta ce dubun dubatan mutane ne suka amsa kiran cocin a ranar Talata na shiga wani jerin gwano a birane da garuruwa inda aka kammala da wani taron addu'o'i.

Da wannan matakin cocin ya nuna a fili rashin gamsuwarsa da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari kan yadda ta kasa magance rikicin manoma da makiyaya da ke janyo asarar rayukan mutane da kuma dukiyoyi. Sai dai dalilin jerin gwanon na wannan karon shi ne kisan gillan da aka yi wa wasu limamin coci biyu da mabiya 17 a wani kauye da ke a jihar Benuwe a watan Afrilu.

Burundi Verfassungsreferendum | Präsident Pierre Nkurunziza
Hoto: Reuters/E. Ngendakumana

Shugaba na dindindin inji jaridar Süddeutsche Zeitung wadda ta leka kasar Burundi tana mai cewa kamar wasu daga cikin takwarorinsa yanzu shi ma shugaban kasar Burundi Pieere Nkurunziza zai kasance kan karagar mulkin kasar har sai Mahdi ka ture.

Jaridar ta ce sakamakon kuri'ar raba gardama kan yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima da aka gudanar a ranar Alhamis da ta gabata, bai zo da mamaki ba, domin tun farko an san yadda za ta kaya. Yanzu dai shugaban zai samu damar ci gaba da mulki har shekara ta 2034. Tun bayan cikan wa'adin mulkinsa na biyu a shekarar 2015.