1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hatsarin jirgin ruwa a Lempedusa

October 6, 2013

Faransa ta bukaci kungiyar EU ta yi nazarin gaskiyar abin da ya wakana don samun mafita a kan hatsarin jirgin ruwan Lampedusa.

https://p.dw.com/p/19uPf
Coffins of victims from a shipwreck off Sicily are seen in a hangar of the Lampedusa airport October 5, 2013. Rough seas again blocked efforts to recover the bodies trapped inside a boat that sank on Thursday, killing an estimated 300 Eritrean and Somali men, women and children who were seeking a better life in Europe. REUTERS/Antonio Parrinello (ITALY - Tags: DISASTER)
Hoto: Reuters

Faransa ta yi kira ga gudanar da taron gaggawa na kasashen da ke cikin kungiyar Tarayyar Turai, bayan mutuwar mutane da dama da ke neman zuwa Turai domin samun mafaka. Mutanen dai sun mutu yayin wani hatsarin jirgi ruwan da ya afku a tekun Italiya. Jirgin dai yana dauke ne da 'yan gudun hijira kimanin 500 daga kasashen Eritriya, da Somaliya da kuma Ghana, wadanda jirgin na su ya tarwatse a tsibirin Lampedusa a ranar Alhamis da ta gabata (03.10.13). Mutane 155 ne kawai suka tsira da rayukansu a lokacin hatsarin, amma har yanzu ana neman sanin makomar kimanin mutane 200, bayan gano fiye da gawarwaki 111. Torokon teku ne ya hana masu ceto kai wa ga wurin da hatsarin ya afku, yayin da jirgin ya kama da wuta, kana ya nitse. Kafofin yada labarai a yankin, sun ruwaito cewar, jami'an tsaron tekun Italiya ba su kai dauki cikin gaggawa ba a lokacin afkuwar hatsarin. Wannan matsuncin, na daga cikin wadanda suka fara kai agaji ga wadanda matsalar ta rutsa dasu:

Ya ce " Ala tilas na dakatar da taimakawa jama'ar, domin abin da doka ta ce shi ne idan na agazawa baki 'yan gudun hijira, to, tamkar ina taimaka musu ketarawa zuwa Italiya. Wannan abu ne da hankali ba zai dauka ba."

Italiya dai ta ce za ta samar da sauye sauye ga dokokin da suka shafi 'yan gudun hijira, inda ta bukaci Kungiyar Tarayyar Turai ta tallafa mata.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Usman Shehu Usman