1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hatsarin jirgin ruwa ya halaka Libiyawa 400

Muntaqa AhiwaApril 15, 2015

'Yan kasar Libiya kimanin dari hudu ne hatsarin jirgin ruwa ya halaka yayin da su ke kokarin tsallakawa zuwa kasar Italiya, yayin da kimanin 480 suka isa tashar ruwan Palermo na Italiya.

https://p.dw.com/p/1F8c8
Symbolbild afrikanische Flüchtlinge im Mittelmeer
'Yan gudun hijira a tekuHoto: picture-alliance/Milestone Media

Lamarin dai ya faru ne ranar Lahadin da ta gabata, kamar yadda wasu da suka tsira da ransu suka tabbatar.

Wani jami'in tsaron gabar kogin kasar Itlaliya, ya ce sun ceto mutane 144 tare ma da gano wasu gawarwaki tara, a hatsarin da aka ce ya faru ne sa'o'i 24 da jirgin ya bar kasar Libiya kan hanyar zuwa Italiya.

Kungiyar shige da fice ta duniya tare da kungiyar samar da agaji ga kananan yara ta Save the Children, sun ce kawo izuwa yanzu akwai mutane 150 da suka tsira, cikinsu kuwa har da yara kanana maza da dama.

Italien Flüchtlinge in Lampedusa
'Yan gudun hijira sun hau layi bayan sauka daga jirgin ruwaHoto: Reuters/A. Bianchi

Wani mai magana da yawun kungiyar shige da ficen ta duniya, Flavio Di, ya shaida wa kamfanin labaran Faransa AFP cewa, jirgin da ya yi hatsarin, yana shake ne da mutanen da basu kasa 550 ba a lokacin da ya nitsen.

An dai danganta wannan lamarin da rikicin kasar Libiya da a yanzu ke tilasatawa mutane tururuwar tserewa zuwa wasu kasashe.

A wani labarin kuma wasu bakin haure kimanin 480 sun isa tashar ruwan garin Palermo na kasar Italiya a cikin jiragen ruwa guda uku. Mutanen da rahotanni suka ce 'yan asalin kasar Somaliya ne a ranar Talata dakarun tsaron iyakokin ruwan kasar Italiya suka ceto su a kusa da gabar tekun tsibirin Sicily. Da sanyin safiyar wannan Larabar kuma wasu bakin haure fiye da dubu daya da dari daya sun isa a yankin.