1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Himma dai Matasa: Mai zanen barkwanci

July 2, 2020

Matashin dai na yin zane-zanen ban dariya da kuma bayar da gudunmawarsa a mujallu da jaridu da sauran kafafen sadarwa, a kokarinsa na inganta aikin jarida ta hanyar hotuna da zane-zane da ke kunshe da wasu bayanai.

https://p.dw.com/p/3eegF
Cartoonist Mustapha Bulama
Mustapha Bulama mai zanen barkwanci a Kadunan NajeriyaHoto: DW/I. Yakubu

Sunan wannan matashin mai sana'ar zanen barkwanci Mustapha Bulama kuma tun bayan da ya kammala karatunsa ya kama sana'ar ta zane-zanen barkwanci, inda ya fara da wata kafar yada labarai mai suna Desert Herald a Kaduna, domin bayar da tasa gudunmawar wajan habaka bangaren ilmantarwa ta hanyar zane-zane masu sanya mutane annashuwa da  kuma bayar da takaitattun bayanai. Ya ce zanen barkwanci abu ne da ya koya tun yana karamin yaro, wanda kuma ke taimakawa ta hanyioyi da dama da ke taimakawa wajan sadarwa ta hanyar zane da sauran rubuce- rubuce masu kai sakwanni ga dinbim masu karanta jarida a kullum.

Karikatur HdM: Kaduna
Zanen da Bulama yai wa jaridar Daily Trust a NajeriyaHoto: Mustapha Bulama

Da wannan sana'ar dai yake rufawa kansa asiri, kuma makudan kudi yake samu ta wannan harkar. Bulama ya kasance daya daga cikin manyan masu zanen barkwanci daga yankin arewacin Niajeriya da ke taka muhimmiyar rawa wajan fargar da al'umma ta hanyar aika takaitattun sakwanni ga masu karanta majallu da jaridu da sauran kasidu da zummar fargar da al'umma. Daga cikin nasarorin da ya samu sun hada da karuwar yawan mutane da yake bai wa horo da kuma yadda duk wanda ya ga zanensa zai yi dariya kuma zai ji hankalinsa ya kwanta. Daga cikin kalubalen da yake fuskanta sun hada da karancin masu wannan fasahar a cikin al'umma da kuma ta rashin kayan aiki da karancin shigowar hukumomi. Burin wannan matashi dai shi ne kara bullo da hanyoyin horar da matasa wannan sana'ar domin masu zane-zane da ke shiga harkar jarida da kuma aikewa da sakonni ta hanyar zanen cikin sauki.