1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tarihi

Hendrik Witbooi: Dan gwagwarmayar Namibiya gwarzon siyasa

Abdullahi Tanko Bala USU
April 4, 2018

Al’ummarsa na kiransa "Nanseb Gaib Gabemab" wato "macijin sari ka noke", Hendrik Witbooi ya hada kan kabilarsa ta Nama wajen bijire wa Jamusawan mulkin mallaka.

https://p.dw.com/p/2vTKB
Symbolbild Namibia
Hoto: imago/Mint Images

Rayuwar Hendrik Witbooi:

An haifi Hendrik Witbooi a 1830 a gundumar Pella, da ke iyaka da Namibiya a yankin da a yanzu yake arewa maso yammacin kasar Afirka ta Kudu. Witbooi ya fito daga tsatson gidan sarautar Witbooi Nama, kabilar makiyaya wadda kuma ke da nasaba da al'ummar Khoikhoi na kudu maso yammacin Afirka. A 1863 al'ummar Witbooi Nama, sun koma wani yanki a kudu maso yammacin Afirka wanda yanzu ya zama kasar Namibiya. A nan Hendrik Witbooi ya sami ilmin zamani a hannun Jamusawa masu yada addini. Daga baya ya koma da zama a cikin tsaunuka a kudu maso yammacin Windhoek, inda ya kafu ya kuma jagoranci al'ummar Nama. Ya rasu a ranar 29 ga watan Oktoba, 1905 a kauyen Vaalgras a wata fafatawa da Jamusawan mulkin mallaka.

 

Shaharar Hendrik Witbooi:

 Ya yi fice saboda kaifin tunaninsa da hanzarinsa na fahimtar illar mulkin mallaka da kuma kiran da ya yi wa kabilun Afirka, wadanda ke gaba da juna su hada kai domin bijire wa Jamusawan mulkin mallaka. Duk da cewa ‘yan kabilar Nama ba su da yawa kuma ba su da makamai isassu idan aka kwatanta da sojojin Jamus, kaifin tunani da kuma dabarun yaki na Witbooi wajen yakar Jamusawa ‘yan mamaya, ya sa ake masa lakabi da "macijin sari ka noke" (Nanseb Gaib Gabemab").

Jamusawa na girmama shi. Shugaban mulkin mallaka na yankin Jamus ta kudu maso yammacin Afirka, Janar Leutwein ya bayyana Witbooi da cewa "Har yanzu ina ganinsa a gabana, mutum mai nutsuwa da kamun kai kuma mai ladabi wanda ba ya kaucewa daga abin da ya dauka aikinsa ko kuma hakkinsa". Witbooi ya yi mu'amala sosai da sauran shugabanni na Afirka da Turai, kuma kungiyar UNESCO ta sanya wasikunsa da kundinsa wadanda aka rubuta da yaren Dutsch a matsayin kundin tarihi na duniya.

 

Hendrik Witbooi ya zama jigon gwagwarmaya:

A yayin da Jamusawa suka mamaye yankuna da dama a kudu maso yammacin Afirka, Hendrik Witbooi ya rubuta wasika zuwa ga sarkin kabilar Herero mai makwabtaka. Duk da cewa kabilar Nama ta fafata kazamin yaki da ‘yan Herero, Witbooi ya bukaci bangarorin biyu su dakatar da fada su hada kai domin yakar ‘yan mulkin mallaka. Wannan kawance ya yi nasara. Jim kadan bayan shekaru goma Jamusawan suka afkawa Herero da Nama a wani kisan gilla da Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana a matsayin "daya daga cikin kisan kare dangi na farko a karni na 20". Sai dai kuma kiran da Witbooi ya yi na hadin kai don bijire wa ‘yan mulkin mallaka ya daukaka martabarsa a matsayin shugaba na kwarai.

 

Dangantakar Hendrik Witbooi da Jamusawa:

A 1893, sojojin Jamus suka kai harin kan al'umomin da ke tsaunukan Witbooi inda suka kashe mutane da dama yawancinsu mata da kananan yara. A bayan wannan ne Witbooi ya sanya hannu a kan yarjejeniyar kariya da Jamusawa. Tsawon shekaru 10 ya hada kai da hukumomin mulkin mallaka, har da samar da makamai ga sojoji domin yakar sauran kabilu. An ruwaito cewa yana da kyakkyawar dangantaka da Janar Leutwein. To amma a 1904 Witbooi ya kaddamar da boren ‘yan kabilar Nama a kan Jamusawan mulkin mallaka, inda ya jagoranci yakin sunkuru tsawon shekara daya kafin a yi masa mummunan rauni.

Hendrik Witbooi: Dan gwagwarmayar Namibiya gwarzon siyasa

Shahararrun kalaman Hendrik Witbooi:

"Ba mu bayar da kasarmu ba, kuma dukkan abin da mai shi bai bayar ba, ba zai yiwu wani ya kwace masa ba."

“Idan wani sarki ya tsaya karkashin inuwar wani, to tabbaci hakika ya rasa ikon kansa, da tasirinsa ko kuma na al'ummarsa da ma kasarsa."

“Kafin rasuwarsa a fagen daga, an ce Witbooi ya yi kiran sulhu. Ya ce ya isa haka nan. Ya kamata yara su samu sukuni."

 

Shin yaya ake tunawa da Hendrik Witbooi?

Har yanzu ana darajantawa da martabar Hendrik Witbooi, a gwagwarmayar samun 'yancin Namibiya (wanda ta samu a 1990). Fuskarsa ta kawata takardun kudin Namibiya na $50, $100 da $200 kuma karfin halinsa na kwatar 'yanci da daukar makamai domin yaki da Jamusawan mulkin mallaka domin kare kasarsa, ana koyar da wannan jajircewa a makarantun Namibiya.

 

Karkashin shirin na musamman da DW kan tsara na Tushen Afirka bisa tallafi na gidauniyar Gerda Henkel.