1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matashiya mai fasa dutse a Adamawa

October 21, 2020

Galibi dai maza ne aka sani da rungumar sana'ar fasa dutse, sai dai a jihar Adamawa da ke Najeriya wata matashiya ta rungumi wannan sana'ar, inda ta shahara tsakanin takwarorinta.

https://p.dw.com/p/3kFDO
Liberian Woman crushing rocks
Matan Afirka na yin sana'ar fasa dutseHoto: Andrew Esiebo

Matashiyar mai suna Hauwa Mohammed dai ta rugumi sana'ar fasa dutsen da aka fi sanin maza da ita, saboda yadda ake yin amfani da karfi wajen yin ta, abin kuma da ake ganin kamar mata ba zasu iya yi ba. To sai dai wannan matashiyar da bayan kammala karatunta, ta bai wa mazan mamaki ta hanyar rungumar wannan sana'ar da a ganinta za ta iya dogaro da ita ba sai ta yi aikin gwamnati  domin samun rufin asirin da take bukata ba.

Hauwa ta bayyana cewa ta samu nasarori a wannan sana'ar da ke biya mata bukatunta. Koda yake akwai kalubalen da take fuskanta. Hauwa ta bayyana muhimmancin sana'o'in hannu ga 'yan uwanta matasa. Abin kuma da masana ke ganin, in har matasan za su tashi tsaye su rungumi sana'o'in hannun, to kuwa za a samu raguwar rashin ayyukan yi.