1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zanga na kara kamari a Hong-Kong

Gazali Abdou Tasawa
June 12, 2019

A Hong-Kong, zanga-zangar adawa da dokar da ke bai wa kasar izinin mika 'yan kasar Chaina mazauna kasar ga hannu mahukuntan Chainar idan sun bukata, ta rikide zuwa tarzoma a wannan Laraba. 

https://p.dw.com/p/3KIZ5
Hong Kong | Protest gegen Auslieferungen nach China & Ausschreitungen
Hoto: Reuters/T. Siu

'Yan sanda a kasar Hong-Kong sun yi amfani da barkonon tsohuwa da kulake da ma harsasan roba wajen tarwatsa masu zanga-zangar da suka yi yinkurin kutsawa a cikin zauren majalisar dokokin kasar inda 'yan majalisar ke shirin nazarin dokar kafin sanya mata hannu. 

Masu zanga-zangar wadanda akasarinsu matasa ne sanye da bakaken riguna da kuma lemomin ruwa sun yi ta dauki ba dadi har ma da bai wa hammata iska da 'yan sandan a gaban harabar majalisar, lamarin da ya tilasta wa Shugaban majalisar dage zaman muhawarar zuwa wani lokaci a nan gaba. 

Sai dai gwamnatin kasar ta Hong-Kong ta ce batun ta janye dokar kamar yadda masu zanga-zangar ke bukata sam bai taso ba. Mahukuntan kasar sun ce 'yan sanda 22 sun ji rauni a cikin fadan