1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Damuwar HRW kan cin zarafin bakin haure

July 7, 2023

Hukumar kare hakkin da Adam ta Majalisar Dinkin Duniya Human Rights Watch ta kira gwamnatin Tunisiya da ta dakatar da gagarumin shirin da ta kaddamar na tasa keyar bakin haure 'yan asalin Afrika izuwa dokar dajin Sahara.

https://p.dw.com/p/4TbmS
Bakin haure a Tunusiya
Bakin haure a TunusiyaHoto: REUTERS

A cikin sanarwar da ta fidda a wannan Jumma'a, hukumar ta ce daruruwan bakin haure da kasar ta kora na can zube a cikin kuncin rayuwa a dokar dajin Sahara a iyakar kasar da Libiya.

Hukumar ta kara da cewa galibin bakin hauren sun fuskanci cin zarafi daga jami'an tsaro kasar a lokacin da suke korarsu, tana mai kiran mahukuntan Tunisiya da su gufarnar da masu hannu a cikin wannan danyen aiki a gaban kuli'a.

A farkon wannan wata ne dai Tunisiyar ta kaddamar da wani gagarumin samame kan bakin haure galibinsu 'yan kasashen Afrika da ke Kudu da hamadar Sahara, biyo bayan korafe-korafe da ta ce ta samu daga al'umma kan yadda bakin haure da yawansu ya kai mutun dubu 21 suka cika kasar.

Wannan shiri dai na Tunisiya na zuwa ne kwanaki kadan bayan cimma yerjejeniya da ta yi da kungiyar EU kan dakile kwararar bakin haure da galibi ke bi ta kasar domin shiga Turai ta barauniyar hanya.