1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

HRW: Sojojin Najeriya sun tsare kananan yara

Uwais Abubakar Idris RGB
September 10, 2019

Human Rights Watch ta gano yadda sojoji suka tsare kananan yara bisa zarginsu da hannu a ayyukan ta’addanci na Boko Haram a Najeriya, lamarin da ta ce ya tauye hakkin yaran.

https://p.dw.com/p/3PLjv
Nigeria Armee rettet Mädchen
Hoto: picture-alliance/dpa/EPA/Nigerian Army

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Human Rights Watch ta fitar da wani rahoto inda a ciki ta ce ta gano yara kanana da sojoji ke tsare da su a matsayin wadanda ake zargi da ayyukan ta’addanci na Boko Haram a Najeriya. Kungiyar ta ce an ci zarafin 'yancin wadannan yara. bincike ya gano munanan halin da ake tsare da wadannan yara kanana a hannun sojojin Najeriyar na tsawon shekaru ba tare da an chaje su da aikata wani laifi ba. Rahoton mai shafuka 50 da ta yi wa take da  ‘’Ba su san suna raye ba ko kuwa sun mutu'' ya bankado abubuwa da yawa na take hakin jama’a  domin ta ce ana tsare da yara ba tare da wata shaidar sun aikata wani laifi ba. 

 

Symbolbild Afrika Kinderbräute
Guda daga cikin yaran ta baiyana halin da suka sami kai ciki na azaba a hannun sojinHoto: picture alliance/AP Images/S. Alamba

Rahoton ya gano cewa daga 2013 zuwa wannan shekarar ta 2019, jami’an sojan Najeriyar sun tsare yara kanana akalla dubu uku da dari shida inda mata suka kasance dubu daya da dari shida da goma sha bakwa. Mafi yawansu kuma ana tsare da su ne a barikin Giwa da ke birnin Maiduguri na jihar Borno. Yaran sheda cewa, an kama su ne bayan da suka gudu daga kauyukansu a sakamakon hare-haren da aka kai musu.Tuni rundunar sojan Najeriya ta fitar da sanarwa inda ta yi watsi da wannan rahoton.

Nigeria Notstand Islamisten Truppen Armee Soldaten
Rundunar sojan Najeriya ta musanta zargin cin zarafin yaranHoto: Reuters

Ko da yake kungiyar ta bayyana cewa an fara samun ci gaba daga matsalar domin daga yara 1900 da ake tsare da su a yanzu an sako mafi yanwansu saura 481, amma duk da haka tana mai bai wa gwamnatin Najeriya shawarar ta kawo karshen tsare yara a gidan yari, maimakon haka ta mika su ga gidan kula da yara na farar hula.