1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumar OIM ta sanar da nutsewar mutane cikin teku

Salissou BoukariSeptember 15, 2014

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta kasa da kasa OIM, ta ce akalla mutane 500 ne suka bace bayan da jirgin ruwan da ke dauke da su ya nutse a tekun Bahar Rum.

https://p.dw.com/p/1DCVR
Bootsflüchlinge vor Italien
Hoto: picture-alliance/ dpa

Hukumar ta OIM ta sanar cewa, wasu 'yan kasar Falasdinu guda biyu da aka samu cetowa, sun tabbatar da wannan adadi, inda suka ce masu yi musu jagora ne suka haddasa wannan hadarin da gangan domin hallakar da su.

Tuni dai humomin kasar Italiya suka soma bincike kan wannan lamari, wanda idan har zargin ya zamana gaskiya, zai kasance nutsewar jirgin da tafi ko wace muni a 'yan shekarun bayan nan, ganin cewa ba hadari ba ne da ya zo daga Indallahi. Mutanen dai sun hada da Misrawa, da Falasdinawa, da 'yan Siriya da kuma 'yan kasar Sudan. Su ma daga nasu bangare, hukumomin kasar Libiya, sun sanar da nutsewar wasu mutane 'yan gudun hijira akalla 200 'yan asalin Afirka a ranar Lahadi a gabacin Tripoli.