1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumar OPCW ta kammala aikinta a Siriya

October 31, 2013

Hukumar da ke kula da yaƙi da makamai masu guba ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta sanar da cewar jami'anta sun bincike wurare 21 bisa 23 da ake harhaɗa makamai masu guba a Siriya.

https://p.dw.com/p/1A9ff
Mideast Syria Chemical Weapons News Guide FILE -- In this Wednesday, Aug. 28, 2013, file photo, a citizen journalism image provided by the United Media Office of Arbeen which has been authenticated based on its contents and other AP reporting, shows members of the UN investigation team take samples from sand near a part of a missile that is likely to be one of the chemical rockets according to activists, in the Damascus countryside of Ain Terma, Syria. The dismantling of Syria's chemical weapons stockpile is under way, but the mission faces multiple challenges, from an ambitious deadline and a raging civil war that threatens inspectors¿ safety. It also has far-reaching political consequences, giving a political boost to President Bashar Assad and further alienating the rebels. (AP Photo/Local Committee of Arbeen, File)
Hoto: picture-alliance/AP

Hukumar OPCW ta ce wurarare guda biyu ne kawai jami'anta ba su sami sukunin kai wa ba garesu saboda dalilai na tsaro.

A cikin watan Satumba da ya gabata Siriya ta amince ta lalata makaman nata, bayan wata yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Amirka da Rasa domin kaucewa kai wa ƙasar hare-hare na taron dangi, dangane da zargin da ake yi mata da yin amfani da makaman a kan farar hula. A gobe ne ɗaya ga watan Nuwamba wa'adin da MDD ta ebawa hukumar domin kammala aikin yake ƙarewa. Kuma nan gaba a ranar 15 ga watan da ke kamawa hukumomin Siriya da na hukumar ta OPCW za su shiga mataki na biyu na aikin lalata makaman masu guba na kusan ton 1000 da Siriya ta ke da shi na makamin Sarin.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu