1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masu takara a jam'iyyun Najeriya sun yi Allah wadai

Zulaiha Abubakar
February 16, 2019

Rahotanni daga Najeriya sun bayyana yadda 'yan takarar shugabancin kasa a manyan jam'iyyu ke cigaba da Allah wadai da sauyin ranar zabe.

https://p.dw.com/p/3DW9A
Nigeria - Verschiebung der Präsidentschaftswahlen
Hoto: Getty Images/AFP/K. Sulaimon

Shugaban hukumar zaben ta Najeriya Mahmood Yakubu ya shaida wa masu sanya ido da wakilan kasashen ketare cewar wannan al'amari ya samu ne sakamakon rashin kyawun yanayin da ya hana jirage dauke da kayan zabe sauka, da kuma gobarar da ta tashi a ofisoshin zabe uku a fadin kasar. Tun da fari magoya bayan Atiku Abubakar mai takarar shugabancin kasar a jam'iyyar PDP, sun zargi shugaba Muhammadu Buhari da masaniya game da wannan danbarwa, kafin daga baya shugaba Buhari ya bayyana takaicin sa game da faruwar wannan al'amari. Inda ya ja hankalin al'umma musamman matasa su guji tada tarzoma saboda banbancin ra'ayin siyasa.