1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukuncin ga jagoran 'yan uwa Musulmi a Masar

Salissou BoukariSeptember 15, 2014

Wata kotu a Masar ta yanke wa jagoran 'yan uwa Musulmi Mohamed Badie da wasu mutane 14 daga ciklin shugabannin kungiyar hukuncin daurin rai da rai.

https://p.dw.com/p/1DCgb
Hoto: Reuters

An yanke musu hukuncin ne a wannan Litinin din bisa kama su da laifin kisa da neman ta da zaune tsaye a wata zanga-zanga da suka gudanar a shekarar bara.

Da farko dai an tsara cewa alkalin zai fara da sauraron shaidu kafin zartas da shari'ar, amma kawai sai alkalin ya shammaci dukkannin wadanda suka zo domin kallon wannan shari'a da ma 'yan jarida, inda nan take ya zartas da wannan hukunci. Da ma dai Mohamed Badie na karkshin wani hukuncin kisa kamar wasu sauran daruruwan membobin kungiyar ta 'yan uwa Musulmi da aka yanke wa hukunci a watan Maris da ya gabata yayin wata shari'a ta kasa da awoyi 24.